SadiQ Sani SadiQ yayiwa Dr Idris Abdul’aziz Bauchi Raddi Mai Zafi kan kiransu Jahilai
Fitaccen jarumi nan na masana’antar kannywood SadiQ sani SadiQ yayiwa Dr . Idris Abdul’aziz Bauchi raddi kan maganganun wanda a cikin bidiyonsa yayi maganganu sosai akan kiransu marar addini wanda yace dole ne ya fito yayi magaana akan wannan ga abinda jarumin yake cewa kamar yadda tashar YouTube mai suna sabuwa Rayuwa na kawo zancen.
A cewar jarumin yace
“Da yake ban fiye magana akan abubuwan da yake faruwa a soshiyal midiya ba amma dalilin haka dole domin ya shafe ni, ya shafi yan uwana yan fim ,ya shafi dangina da ‘ya’yana da duk wani dan uwana
A yan kwanaki ina cikin manhajar Tiktok ina ganin wasu videos na malamai suna sanya da rigar malanta suna saman mimbari suna fadin maganganu akan yan uwansu malamai wanda a nawa gani wannan kuskure ne a nawa tunanin a nawa fahimta ana kallon su a matsayin malamai na addinin musulunci, addinin da yake koyar da tarbiyya addinin da yake koyar da ya kamata amma suna amfani da wannan suna aikata abinda zai sanya ana kallon addini ta wata fuska ta adaban wanda hakan baida ce ba.
“A ciki akwai wani malami na yarda da nagartasa da iliminsa na addini wani mutumin bauchi sai naji yana kiran wani dr jaki na dusten tanshi lallai wannan sunan baimin dadi ba da naji wani yana kiran dan uwansa da dr jajji da ina da hali ina da iko naga wannan malami sai nace bai kyauta ba.
Bayan yan kwanaki naga wannan malamin da ake kira Dr jaki yana baje wasu manya manyan malaman addini na tabbata sun fushi ilimi sun fishi nagarta sun fishi kusan ci da Ubangiji ma a cikin malaman da ya rinka bajewa Akwai Dr.Ali pantami, Sheikh Dahiru usman bauchi da dai sauransu.”
Ina alfahari da ni dan fim ne har mahadi ya bayyana na mutu na kowa Ubangiji na kuma na tashi a gaban Allah naje a matsayin dan fim in sha Allahu bana nadama, ban taba nadama da cewa ni dan fim bane koda da rana daya.
Sadi sani sadiq ya kara da cewa na ya daina zagin malaman da suka fishi saboda neman suna suke fishi suka fishi har a gurin Allah.
Dan Allah ka daina abinda kake ba dai dai bane.”