Labarai

Sai da na shafe shekaru 3 a asibiti saboda gudun wasu mutane da suke son hallaka ni kawai dan an haifeni babu hannuwa – Inji wata mata mai nakasa

Wata mata mai bukata ta musamman, ta bayyana yadda wadansu mutane suka dinga kokarin hallaka ta kawai domin an haifeta babu hannaye. A wata hira da tayi da gidan talabijin na Afrimax Tv, ta bayyana cewa, ita haifaffiyar wani kauye ce da yake kusa da babban birnin Nairobin kasar Kenya.

An haifeta babu hannaye biyu

Sai da na shafe shekaru 3 a asibiti saboda gudun wasu mutane da suke son hallaka ni kawai dan an haifeni babu hannuwa – Inji wata mata mai nakasa
Sai da na shafe shekaru 3 a asibiti saboda gudun wasu mutane da suke son hallaka ni kawai dan an haifeni babu hannuwa – Inji wata mata mai nakasa

Ta bayyana cewa, lokacin da aka haifeta, likitocin da suka karbi haihuwar ta, sun girgiza sakamakon ganin jaririya babu hannaye guda biyu. Sai aka ajiye ta a asibitin har na tsawon shekara uku, saboda a cewar su Idan aka kai ta kauyen su, al’ummar kauyen baza su karbeta a matsayin mutum ba, kasantuwar bata da hannuwa. Labarunhausa na ruwaito

Maryam taci gaba da cewa,

“haka na taso na girma a cikin al’ummar da a ko da yaushe burin su shine su hallaka ni, kawai saboda bani da hannaye. “

Yadda wadansu mutane suka kusa kashe ta

Ta kara da cewa,

“akwai ma wani lokaci da wadansu mutane suka kusa kasheta, lokacin da mahaifiyar ta, ta je da ita bakin kogi domin ta debi ruwa. Sun dilmiya mahaifiya ta cikin ruwa, amma saboda ta iya ninkaya, sai ta yi ta yin iyo har ta tsallaka daya gabar kogin, kuma ta fito ko kwarzane babu a jikin ta.”

Mahaifin ta ya gudu

A fadar ta, bata san mahaifin ta ba, saboda tunda aka haifeta a haka, bai taba ziyartar su ba. Kakan ta na wajen uba, shine wanda ya raineta kuma yana matukar kaunar ta kamar yadda ta fada. Ya taka mahimmiyar rawa wajen kawowar ta har izuwa yanzu a raye, wanda da badan shi ba da tuni an kasheta.

Bugu da kari Maryam tace, da kafar ta take yin mafi yawan cin abubuwan rayuwa na yau da kullum, kamar su wanki, rubutu da kuma shafa kayan kwalliya, duk da kafa take yin su.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button