Kannywood

Buri na a yanzu na goga kafada da manyan mata jarumai na duniya -Hauwa S Garba

Daya daga cikin jarumai mata a masana’antar Kannywood wadda a yanzu tauraruwar ta ke haskawa, Hauwa S Garba, wadda a ka fi sani da suna Mama a cikin masana’antar, wadda a farkon wannan shekarar za a iya cewa ita ce mace da ta shirya fina-finai manya har guda uku, wadanda su na shirin fitowa a ka shiga matsalar Covid-19.
Wakilin mu ya nemi jin ta bakin ta dangane da halin da ta ke ciki da kuma yadda a ka yi ma har ta zama Furodusa a daidai wannan lokacin da a ke ganin kamar harkar ta mutu.

Amma dai ita a wajen ta harkar ta na nan ba ta mutu ba, domin kuwa kowa lokacin sa ya ke ci a yanzu, ta fara mana da cewar.

“To ni dai a yanzu zan iya cewa da kai ban fuskanci wata matsala ba, domin kamar shekaru biyu da su ka wuce an saka ni a fina-finai da dama kuma a lokacin ma ban yi wani tunanin yin fim na kaina ba, amma a yanzu da na samu dama duk da halin da a ke ciki ina yin fina-finai nawa na kaina. Domin na shafe shekaru biyar a cikin harkar nan, a yanzu da damar ta zo min, sai na ga to me ya sa ba zan yi nawa na kaina ba, saboda a halin ma da a ke ciki a yanzu na yi na daya na yi na biyu, na yi na uku har ma an kammala su duka. Da farko na yi Babban dalilin, sai Abun al’ajabi, da kuma wanda a ka gama yanzu, ko ba komai dai a yanzu, zan iya cewa na motsa daga matsayin jaruma na shiga sahun masu shirya fina-finai na kan su”.

Tun da Hauwa S Garba ta kai ga wannan matsayin ko me ta tsara wa rayuwar ta?

“To ni abun da na tsarawa rayuwa ta shi ne, ina tunanin na yi fina-finan da na yi a baya a matsayin jaruma, to na yi ma ya fi haka yawa. Haka ma a bangaren Furodusin nan ma ya zama na bunkasa, babban buri na, domin na zama cikin matan da duniya ta sanni a cikin harkar fim”.

Ko akwai wata sana’a ko kasuwanci da Hauwa S Garba ta ke yi bayan harkar fim?

“Eh gaskiya ne ina yin harkar kasuwanci irin na fitattun jarumai a duniya, domin ka san ‘yan fim kasuwancin su ba ya wuce kayan kwalliya, saboda harkar fim ta kwalliya ce, shi ya sa za ka ga duk kasuwancin na mu na kayan kwalliya ne, domin haka ina da wata sana’a ta daban a bayan fage”.

Me sakon ki ga abokan sana’ar ki?
“Ni sako na ga abokan sana’ar mu ta fim shi ne, su sani komai lokaci ne, idan wani Furodusa ko Darakta ya ce ba zai yi aiki da kai ba, to Kar ka damu, Kar ka ji komai a ranka, kai ma za ka iya yi, domin ko ni abun da ya sa na yunkura har na zama Furodusa abun da ya faru a gare ni kenan a shekarar da ta gabata akwai wani aiki da za mu yi, to ba ma shiri da Furodusan, duk da ni ban san abun da na yi masa ba, da a ka kirawo ni aikin sai ya ce, ba zai yi aikin da ni ba har sai na kira shi na ba shi hakuri, ni kuma na ga ban san abun da na yi masa ba, domin haka ba zan ba shi hakurin ba, na san ‘yanci na. Wannan ta sa ni ma na ga cewar tun da ina da dama kawai bari na fito na fara yin Furodusin din, domin haka mutane su sani komai lokaci ne, idan lokacin mutum ya zo sai a tafi da shi”. A cewar jaruma Hauwa S Garba.

#northflix

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button