Labarai

An harbe ƙasurgumin ɗan fashin jeji, Ibrahim Chire a Zamfara

Dakarun sojin Najeriya da ke aiki da ‘Operation Hadarin Daji’ sun kashe ɗaya daga cikin gawurtattun ƴan fashin daji da suka yi kaurin suna a Zamfara.

Daily Trust ta rawaito cewa kwamandan ƴan bindigan da aka bayyana sunansa da Ibrahim Chire, ya addabi yankunan Gando, Gwashi, Bukkuyum da Anka.An harbe ƙasurgumin ɗan fashin jeji, Ibrahim Chire a Zamfara

Darakta mai kula da ayyukan yada labarai na tsaro, Maj.-Gen. Must Danmadami, a wata sanarwa da ya fitar a daren ranar Alhamis, ya bayyana cewa an kashe dan ta’addan ne a yayin wani artabu da sojoji suka yi.

Ya ce an kuma kashe wasu ƴan ta’adda biyu yayin da mabiyansu suka gudu da raunukan harbin bindiga.

Danmadami ya bayyana cewa, “Rundunar Operation HADARIN DAJI sun gudanar da sintiri na yaki da ‘yan bindiga a dajin Doka da ke karamar hukumar Anka a jihar Zamfara a yau 20 ga watan Oktoba 2022.

“A lokacin da suke sintiri, sojoji sun afka wa ƴan ta’adda kuma sun yi ta harbi. Dakarun da ke aikin sun kashe ‘yan ta’adda biyu yayin da wasu kuma suka gudu da raunuka.

“Lokacin da ake bincika yankin gaba daya, an gano daya daga cikin ‘yan ta’addan da aka kashe da sunan Ibrahim Chire, wani shahararren shugaban ‘yan bindiga da ya shahara wajen ta’addancin Gando, Gwashi, Bukkuyum da Anka.”

Ya kara da cewa daga baya sojojin sun kwato AK 47 daya, da harsashi mai girman 7.62mm, Babur daya, wayoyin hannu da dai sauransu.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button