Labarai
Mai magana da yawun Tinubu zai dakatar da aikinsa


Advertisment
Mai bai wa shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai, Ajuri Ngelale ya sanar da ajiye muƙaminsa.
Cikin wata sanarwa da Ngelale ya wallafa, ya ce a ranar Juma’a ya miƙa takardar ajiye aikin nasa zuwa ga shugaban ma’aikata na fadar shugaban ƙasa, Femi Gbajabiamila.
”Na yi hakan ne domin samun isasshen hutun da zai ba ni damar mayar da hankalina kan matsalolin rashin lafiya da iyalaina ke fuskanta”, in ji Ngelale.
Mista Ngelale ya kuma ce ya sauka daga duka sauran muƙaman da yake riƙe da su.
Sauran mukaman sun haɗar da wakilin shugaban ƙasa na musammman kan sauyin yanayi da kuma shugaban kwamitin shugaban ƙasa kan inganta muhalli.