

Kyaftin din kungiyar kwallon kafa ta kasa Super Eagles Ahmed Musa, Ya bayar da gudunmawar kudi naira Miliyan Biyu (#2,000,000) domin gina masallaci a harabar makarantar sikandire ta Bokavo Barrack da ke Kano.
Ahmad Musa wanda tsohon dan wasan gaba na CSKA Moscow ne ta kasar Rasha ya bada gudunmawar ne bayan ziyar tar makarantar da ya yi bayan kammala atisaye da kungiyar Kano pillas da yammacin jiya.
Hakazalika musa ya yi alkawarin bayar da gudunmawar gyaran kujerin zama da suke makarantar.
Da ya ke ganawa da manema labarai Musa ya kuma yi kira da mahukunta a makarantar da su cigaba da gudanarda abunda ya kamata domin gyaruwar al’amuran makarantar da hakan zaisa al’umma da dama suyi kwadayin sanya ‘ya ‘yansu a makarantar don samun ilimi addinin Musulunci a fadin yammacin arewacin Nigeriya.
Hutudole na ruwaiti wannan labari da ya ke jawabi ya yin karbar gudunmawar kudin, Daraktan makarantar Alhaji Yusuf Sa’idu ya nuna farin cikinsa da ziyarar da Ahmad Musa ya kai makarantar, da sakamakon zuwan nasa ya bada tallafin kudi, muna yi masa addu’ar fatan Alkhairi a rayuwarsa.
Sannan Alhaji Yusif ya kuma ce ziyarar Musa ta zo a daidai lokacin da suke bukatar gudunmawa, bayaga lissafa masa irin tarin matsalolin da suke cin karo da su ciki harda rashin ingancin ginin Masallacin da bandaki da rashin ajujuwa da kujerun zama a wasu daga cikin ajujuwan makarantar.