Labarai

‘Yan kungiyar IPOB sun kashe sojin Najeriya mata da mijinta, kuma sun yanke kawunan su a jihar Imo

‘Yan bindiga sun kashe wasu ma’auratan sojoji mata da mijinta har lahira, kuma suka yanke kawunan su.

Wata majiya daga rundunar sojojin ta shaidawa jaridar Sahara Reporters cewa jami’in sojan A.M Linus mai mukamin ajin farko na saja, da matar tasa suna kan hanyar sune ta zuwa jihar Imo, yayin faruwar lamarin.

Sun kira iyalan mata da mijinta suna yi musu dariya

Bayan sun datse kawunan mamatan, yan bindigar sun kira iyalan su, inda suka dinga yi musu dariya. A bidiyon da SaharaReporters suka gani, wanda yayi faca-faca da jini, anga ‘yan bindigar suna dora kawunan akan kirjin mamatan, bayan faruwar lamarin.

“Abin bakin cikine, ace mu kanmu sojoji bamu tsira ba. Mutumin da aka kashe shine mai lamba 19 a cikin rukunin cikakkun sojoji da aka dauka, matarsa kuma ita ce ta 79RL.

” Suna kan hanyar sune ta zuwa jihar Imo, ranar Lahadi, yayin da lamarin ya faru. Za ku yi mamaki, idan kukaji cewa daga baya ‘yan bindigar sun kira iyalan mamatan suna zolayar su, tare da yi musu barazanar suma zasu kashe su.

” Mamacin yana da mahaifi da ya rage, kuma danuwansa ma soja ne, da yake aiki a wata bataliya, a jihar Kaduna. Ita kuma matar, sai da ‘yan bindigar suka yi mata fyade kafin su kashe ta “.

Kamar yadda Jami’in sojan ya shaidawa jaridar Sahara Reporters. 

mata da mijinta
‘Yan kungiyar IPOB sun kashe sojin Najeriya mata da mijinta, kuma sun yanke kawunan su a jihar Imo

Hare-haren masu dauke da makami, yana kara ta’azzara, a yankin kudu maso gabashi, a ‘yan kwanakin nan, inda hare-haren sunfi mai da kai ne akan jami’an tsaro da kuma kadarorin gwamnati.labarunhausa na wallafa a shafinta

Harin baya-bayannan, shine wanda maharan suka yiwa wani shingen bincike, dake  karamar hukumar  Agulu, Anaocha ta  jihar Anambra tsinke, inda suka bude wuta akan jami’an soji, wanda suka kashe soja daya.

Haramtacciyar kungiyar IPOB, masu rajin kafa kasar Biafra, sune ake zargi da kai hareharen da ake asarar rayuka a yankin, inda ko da yaushe suke musanta hannu a cikin badakalar kai hareharen.
Shugaban kungiyar ta IPOB Nnamdi Kanu, a halin yanzu, yana tsare a Abuja, inda yake fuskantar tuhuma akan cin amanar kasa.labarunhausa na tattaro bayyanai

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button