Kannywood
[Bidiyo] Duk randa Allah zai dauki ran Maryam Yahaya ina rokonsa ya dauka tare da nawa, Matashi
Advertisment
Wani matashi wanda ya bayyana kaunar da yake yiwa jarumar Kannywood, Maryam Yahaya a fili ya ce ba zai iya rayuwa a duniya ba idan jarumar bata raye.
Da haka ne yace yana fatan Ubangiji ya dauki rayuwarsa a ranar da zai dauki rayuwar jarumar.
A wani bidiyo na TikTok da matashin , an ga matashin yana bayyana sirrin da ke ransa.
Ya fara ne da cewa:
Advertisment
“Hakika, gaskya ni bazan iya rayuwa babu Maryam Yahaya ba, ba wai kuma ina nufin a karkashin inuwata ba.
“Ba zan iya rayuwa ba muddin bana jin motsinta, ko da a birnin kif take. Shiyasa a ko da yaushe nake addu’a, duk ranar da Allah ya tashi daukar ran jaruma Maryam Yahaya, to ya dauka tare da nawa.
“Saboda idan babu Maryam babu ni.”
Ga bidiyon: