Wani dan kasar Mexico ya daura aure da kada cikin armashi da ban sha’awa
Wani magajin gari a kasar Mexico ya auri wata kada sanye da rigar aure, inda ya sumbaceta a mastayin cikar sigar aure.
Yana daga cikin tsohuwar al’adar ƴan asalin ƙasar, wanda Victor Hugo Sosa ya jagoranta, kuma ya kudurin aniyar kawo wadata a ƙauyen San Pedro Huamelula a kudu maso yammacin Mexico.jaridar Labarunhausa na ruwaito
Ana wa kadar lakabi da Gimbiya
Kadar mai shekaru bakwai ta kasace mutanen garin na yi mata lakabi da ‘yar karamar Gimbiya, inda suke kallon ta a matsayin wata abar girmamawa mai wakiltar uwa ta duniya; Auren da shugaban wannan gari yana nuna haɗewar mutane da wannan dabba madaukakiya.
Bikin anyi shagali
Bikin ya kayatar da kade-kade da wake-wake, da raye-rayen gargajiya yayin da aka umurci ango da ya sumbaci sabuwar amaryarsa.
An yi ta kade-kade da ganguna a lokacin da mai unguwa ya dauki amaryar sa a hannunsa suna kewaye yayin da maza ke ta musu fifita da hulunan su.
An daure kadar dan gudun cizo
An daure bakin kadar don gudun kar ta ciji ango a lokacin da zai sumbace ta,inda ya sumbace ta sau ba adadi.