Labarai

Jibwis Ta Yabawa Hukumar Sojoji Kan Zartar Da Hukunci Ga Makasan Gwani Aisami – Sheikh Dr.Abdullahi Bala Lau

Kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah wa iqamatis sunnah ta tarayyar Najeriya ta yabawa hukumar sojojin Najeriya wajen zartas da hukunci na kora ga ‘yan ta’addan Sojojin da suka yiwa marigayi Sheikh Gwani Aisami kisan gilla a kwanakin baya a garin Gashua ta jihar yobe.

Jibwis Ta Yabawa Hukumar Sojoji Kan Zartar Da Hukunci Ga Makasan Gwani Aisami - Sheikh Dr.Abdullahi Bala Lau
Sheikh Gwani Aisami Allah ya Jikanka yayi maka Rahama

Shugaban JIBWIS Sheikh Dr. Abdullahi Bala Lau, shi yayi wannan furuci a wata takarda da ya fitar ga manema labaru a ofishinsa dake birnin tarayya Abuja.
Shehin Malamin yace “zamuci gaba da bibiyar shari’ar da zata gudana a kotu domin ganin an tabbatar da anyi musu shari’ar da ta dace da su a hukumance” Inji shi.
Kuma mun yaba da hukuncin da hukumar soji tayi wajen gaggauta mai dasu kurata, wato ta kwace mukamansu na soji, ta kuma kore su daga aiki cikin kankanin lokaci.

Wannan kungiya mai albarka a kullum takan yi kira ga mabiyanta ta a zauna lafiya, a guji tashin hankali, kuma baza mu zuba ido ana kashe malaman mu da dai-dai da dai-dai ba. Har yanzu ciwon da aka mana na kisan Marigayi Sheikh Ja’afar da marigayi Sheikh Auwal Albani ba, bamu warke ba ga kuma na Sheikh Gwani Aisami ya zamar mana sabo fil.

Dan haka muna kira ga hukuma data dinga daukan mataki ga makasan in an kama su, wannan shi zai kawo karshen wannan ta’addanci ga malaman mu a fadin kasa insha Allah.

✍️Ibrahim Baba Suleiman

JIBWIS NIGERIA

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button