Labarai

Gwamnati ta kori alkalin da ya raba auren wani mutum, daga baya ya koma ya dirkawa matarsa ciki

Gwamnatin Jihar Legas ta kori alkalin wata kotu, Ishola Adeyemi, wanda ake zargin ya raba auren wani da ya kawo kara, Olayemi Ayeni kuma ya koma ya kwace matarsa, Premium Times ta ruwaito.

Lamarin ya bayyana ne bayan wani bidiyo ya bayyana a shafin Facebook din nishadantarwa na “Ogbongefrienda” a 2016 ya yi ta yawo.

Sai dai babu wanda ya fahimci bidiyon da kyau, wanda aka wallafa shekaru shuda su ka gabata a kafar sada zumunta, sai dai ya bazu sosai.

A bidiyon wanda ya yadu, Ayeni ya bayyana yadda Alkalin, Adeyemi, wanda ya ke zargin matarsa, Doyin Okububi, ta kwanta masa a rai ya raba aurensu kuma ya hana shi damar rike yaransa.

Bidiyon da ya yadu

A cewarsa ya fara fuskantar tashin hankali ne bayan matarsa ta dena daraja shi bayan ya bata Naira miliyan biyar ta ja jari.

Mai korafin ya ce matarsa ta kwashe kayanta ta bar gidansa sannan ta kama wani gida kusa da nashi.

A cewarsa:

“Na samu matsala da matata, ta kwashe kayanta ta bar gidana sannan ta kama wani gidan kusa da nawa. Na bata Naira miliyan biyar don ta ja jari ta bude wata makaranta mai suna Greatest Kiddies Foundation. Wannan sana’ar ta janyo min matsala wanda na kasa ci gaba da iya tankwasa ta.”

Ya zargi alkalin da yayi shari’a tsakaninsa da matarsa da tilasta saki tare da dirkawa matarsa ciki.

“Bayan nan da watanni goma, na yi tunanin aurenmu zai iya gyaruwa ta hanyar sasanci. Alkalin, Dr Ishola Azakiq ya yi gaggawar raba aurenmu sannan ya dirka mata ciki bayan watanni 3 da raba aurenmu,” a cewarsa.

A bidiyon, Ayrni ya zargi alkalin da tura masa ‘yan sanda don su kama shi su kuma tura shi gidan yarin Kirikiri da ke Jihar Legas.

Cikin radadi yake bayyana cewa yanzu haka cikinta ya kai tsufar watanni tara, kuma na alkalin ne.

“Abinda ya fi damuna shi ne hana ni damar ganin yarana da mutumin yayi. Dakyar nake samun damar ganin yarana su ma a harabar makarantar. Yanzu kuma yaran su na karkashin kulawarsa; ya ci gaba da kula da kasuwancin da na ba matar jari. Ya hanani damar ganawa da yarana sannan ya dirkawa matata ciki tare da tura ni gidan yari,” inji mutumin.

Ya ci gaba da cewa yana so yaransa su dawo karkashin kulawarsa don ba ya son su tashi cikin rashin tarbiyya. Yana da hakinsa kuma zai iya tura su makarantar kwana. Ya bukaci taimakon ‘yan Najeriya a cikin bidiyon don su kwatar masa hakkinsa.

Gwamnatin Jihar Legas ta dauki mataki

A wata takarda ta ranar Talata wacce gwamnatin Jihar Legas ta saki ta ce:

“Tsohon alkalin kotun ya yi amfani da ofishinsa wurin yin abinda bai dace ba tare da nuna rashin sanin makamar aiki dangane da mutumin da ya kawo karar matarsa. Ya kwace matar tare da yaransa daga wurinsa.”

Sakataren gwamnatin jihar na hukumar DSVA, Titilola Vivour-Adeniyi, ta saki takardar.

A cewarta, hukumar shari’ar Gwamnatin Jihar Legas ta yi bincike akan lamarin da ya auku ne tsakanin shekarar 2014 da 2015. Kuma abubuwan da ta gano ya sanya ta kori alkalin daga aiki.

© Labarunhausa

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button