Labarai

SSS sun dira a CBN sun kuma mamaye ofishin Emefiele

Jami’an hukumar tsaro ta farin kaya, SSS sun mamaye hedikwatar babban bankin Najeriya, CBN inda suka kwace ofishin gwamnan babban bankin kasar Godwin Emefiele.

SSS sun dira a CBN sun kuma mamaye ofishin Emefiele
SSS sun dira a CBN sun kuma mamaye ofishin Emefiele

Jaridar DAILY NIGERIAN ta rawaito cewa a kwai wata jiƙaƙƙiya tsakanin jami’an SSS da Emefiele kan zargin tallafawa ta’addanci.

A baya dai hukumar ta SSS ta nemi kotu ta bata izinin kama Emefiele amma ya fice daga kasar domin hutun shekara da zai kare a gobe 17 ga watan Janairu.

Sai dai a watan Disamba ne babbar kotun birnin tarayya ta haramtawa SSS kama, gayyata, ko kuma tsare Emefiele.

Amma kuma a yau Litinin da jami’an SSS da suka isa hedikwatar ta CBN, sun shigo da motoci kusan 20 dauke da jami’an tsaro.

Jami’an sun kuma hana duk ma’aikatan bankin shiga ofishin Emefiele.

Peter Afunanya, mai magana da yawun SSS, har bai amsa sakon neman bahasi da wakilin Daily Nigerian ya aike masa ba.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button