Tallafin da Aishatul Humaira ta ba wacce ta musulunta a TikTok ya janyo cece-kuce
Tashar Tsakar Gida ta bayyana yadda wata baiwar Allah ta musulunta a kafar sada zumuntar zamani ta TikTok a makon da ya gabata ta hannun wani ma’abocin da’awa ta kafar, Abu Salma, Tashar Tsakar Gida ta ruwaito.
Ya yi bidiyo ne inda ya bayyana inda ta karbi kalmar shahadar da kuma irin taimakon da ta samu daga wurin mutane daban-daban wanda take bukata don ci gaba da addininta cikin salama.
Kamar yadda Abu Salma ya bayyana, yanzu haka an samu masu riketa har mutane biyu baya ga sauran tallafin da ta samu har Jaruma Aishatul Humaira ta Kannywood ta yi mata alkawarin sama mata aiki mai albashi mai tsoka kamar yadda Abu Salma ya karanta sakonta tare da yi mata godiya da fatan alkhairi.Via
Sai dai saboda caccakar da Abu Salma ya dade yana yi wa ‘yan fim akan cewa ko da sadaka suka yi da kudin fim Allah ba zai karba ba an yi caa akansa inda kowa ke tofa albarkacin bakinsa.
Ganin caccakar da ya saba, da kuma yadda ya fito yana yaba wa Aisha tare da yi mata addu’o’i da fatan alkhairi ne ya janyo mutane suka dinga sukarsa.
Sai dai daga baya Abu Salma ya fito yayi bayani inda yace ko da arne ne ya baka kudi duk da baya da lada, idan kaci, ka ci halas balle kuma ita Humaira ba kudi ta bayar ba, aiki ne zata samar wa wannan wacce ta musulunta.