Mutane Da Yawa Sun Musulunta Saboda Kallon Shirin Izzar So – Lawan Ahmad
A wani rahoto da muka samu furodusan fim din ‘Izzar So’ Lawal Ahmad ya bayyana cewa dalilin fim ɗin sa ‘Izzar So’ mutane na ta musulunta saboda karantarwar da ke kunshe a cikin sa.
Lawal ya bayyana wa majiyarmu jaridar Premium Times a hira da yayi da jaridar cewa fim ɗin ‘Izzar So’ fim ne da ke karantar da abubuwan da manzon Allah, SAW ya umarci musulmi su yi a rayuwar su.
Ya kara da cewa fim ɗin yana koyar da tarbiyya, da kuma bin dokokin addinin musulunci.
” Son Annabi da karantar da abinda ya koyar shine muke nuna wa a fim ɗin ‘Izzar so’. Babban abinda muka fi maida hankali a kai shine karantarwar Annabi SAW.
” Ina so in sanar muku cewa dalilin wannan fim ‘Izzar So’ ni da kai na na musuluntar da mutane, baya ga wasu da aka musuluntar wanda aka sanar dani. Dukkan su kuma saboda irin karantarwar da muke nunawa a fim ɗin.
Lawal Ahmad, ba ɓoyayye bane a farfajiyar funafinan Hausa na Kannywood.
Yana daga ciki fitattun jarumai da suka daɗe a farfajiyar kuma ya goya sabbin jarumai da dama.
Zuwa yanzu ‘Izzar So na daga cikin fim din da ak fi kallo a shafin YouTube dake yanar gizo.
Ana saka ‘Izzar So’ a tashar Bakori TV dake YouTube wanda ke da mabiya sama da 900,000. Sannan a duk lokacin da aka saki cigaba da wannan fim ‘Izzar So’ aka samu sama da mutum 700,000 dake tsinduma cikin shafin YouTube domin su kalli wannan fim ɗin.
Wani daga cikin masoyan wannan fim mai suna Ahmed Musa, ya bayyana wa wakilin mu cewa yana ƙaruwa matuka da wannan shiri na ‘Izzar So’.
” Tabbas ina kallon wannan fim, a duk lokacin da aka sake shi. Fim ne mai ma’anar gaske. An tsara shi ta yadda duk wani mai kallo zai karu, sannan ya na gyara tarbiyya da kuma karantarwar Annabi SAW game da tarbiyya da mu’amular rayuwa.