Safara’u SAFAA ta baiwa yan fim hakuri tare da Nadama a rayuwarta
Safiya Yusuf wadda akafi sani da Safara’u a cikin shirin nan mai dogon zango na Kwana Casa’in a shekarun baya, Jarumar wadda a kwanakin baya babu maganar da akeyi sama da tata,kafin daga bisani aka kama Iyayen gidan ta a kasar Niger (Mr 442 da Ola Of Kano).
Tun bayan kama su 442 dinne dai, jarumar ko kuma muce mawakiyar aka nemeta aka rasa wajen ganin bidiyoyin ta na rashin da’a.
Safara’u din ta bayyyana kalaman ta na dama ne da kuma bawa Abokan aikin ta na Kannywood hakuri ne a hirar da sukayi da fitacciyar jarumar nan ta Kannywood Yar asalin kasar Gabon,wato Hadiza Gabon cikin shirin ta mai suna Gabon Talk Show.
Jarumar ta bayyana abubuwa da dama a cikin hirar,ta bayyana abunda ya faru da ita da 442,da kuma batun sakin bidiyon Tsaraicinta da aka tabayi a sherkarun baya.
Zaku iya amfani da link na kasa domin kallon wannan hirar.