Labarai
Sojoji sun gano wata ‘yar makarantar Chibok da aka sace tare da jaririnta a Borno
Advertisment
Sojojin Najeriya sun gano wata Hauwa Joseph, wadda a cewarsu tana daya daga cikin ‘yan matan da aka sace daga makarantar Sakandaren ’yan mata ta gwamnati da ke garin Chibok a Jihar Borno a ranar 14 ga Afrilu, 2014.jaridar LIB na ruwaito
Rundunar sojin a cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafukanta na sada zumunta a ranar Alhamis, 16 ga watan Yuni, ta ce an gano Hauwa da jaririnta a wani samame da suka kai a Borno.
“Sojoji yayin aikin share fage a ranar 14 ga watan Yunin 2022 sun kama wata yarinya da aka sace daga GGSS Chibok mai suna Hauwa Joseph, wadda Boko Haram suka yi garkuwa da ita a ranar 14 ga watan Afrilun 2014. Yarinyar Chibok da aka kama tare da jaririnta a halin yanzu suna wani asibitin sojoji.” sanarwar ta karanta.


![[Bidiyo] Ni na haɗa auren G-Fresh da Alpha Charles – Jaruma Babiana](https://i0.wp.com/hausaloaded.com/wp-content/uploads/2024/12/Picsart_24-12-25_12-05-31-313-scaled.jpg?resize=220%2C150&ssl=1)




