Ta Fadi Dalilinta Na Kulle Saurayinta A Kwalba
Wata budurwa ‘yar shekaru 19 data kamu da soyayyar wani saurayi mai shekaru 21 da haihuwa ta fadi dalilinta da ya sakata har ta yiwa saurayin nata asirin da aka kulle masa shi a kwalba.
Bayan da ‘yan uwa da abokan saurayin suka fahimci ya sauya daga yadda yake da. Inda nan da nan ransa ke baci yayi ta farfasa duk wani abunda ke tare da shi komai darajarsa ko tsadarar abun, yasa suka tsargu suka tuhumi budurwar tasa.Tonga abdul Tonga na ruwaito
A yayin da budurwa take maida musu gaskiyar abunda ya faru, tace ita dai naje waje bokaye ne da suka mata asirin da zata saka saurayin nata a kwalba saboda ya rika yin duk abunda take so da shi. Tace kuma ita tayi hakan ne da kyankyawan niyar kada wata mace ta rabata dashi. Amma ita batayi bane saboda ya rika lalata abubuwa ba.
Bayan data fito da maganan a fili ne iyayen yaron suka nemi ta kaisu wajen wanda ya mata aikin domin neman yadda za a cire musu dansu daga cikin kwalbar soyayar da aka cusa shi.
Yanzu dai muna jiran mu samu labarin yadda zata kaya ko za a dace ko kuma shikenan dan nasu zai gama rayuwarsa a hakan.
Samari sai ayi hatta, mace idan tana sonka zata iya yin komai akanka. Haka nan idan tana kinka tana iya yin komai. Da fatan baza a fada hannun masoyan da zasu cutar ba.
Wasu Abubuwan Dake Sa Ma’aurata Shakuwa Da Juna
Akwai wasu dabi’u da mu’amalolin da kan iya sa ma’aurata su shaku da junansu har guda ya kasa nisantar guda sai abunda ya zama dole
Ga wasu abubuwan da suke iya sa ma’aurata shakuwa matuka a junansu.
1: Cin abinci, safe dana dare tare.
2: Sallolin farilla tare.
3: Fita sayayya ko yawon shakatawa tare
4: Yiwa juna ba’a da Barkwanci.
5:Kallon wani shirin na talabijin tare.
6: Tilawan Alkurani tare.
7: Zuwa Gaisuwa ko dubiya tare.
8: Yin wasannin game tare.
9: Zuwa Aikin Hajji, Umrah ko wata kasar tare.
10: Kwanciya a shinfida guda tare.
Babu shakka duk ma’auratan da suka saba yin wadannan abubuwan tare, tabbas zasu shaku da junansu.