Labarai

Wani Karin Haske Game Da Dibar Sabbin Ma’aikatan Shirin N-POWER BATCH C 2020

Advertisment

Muna samun tambayoyi game da shin me shaidar kwalin SSCE zai iya cikewa?

Ga yadda tsarin N-power yake :

1- N-power Agro
2- N-power Tax
3- N-power Build
4- N-power Health
5- N-power Teach
1- N-power Agro:

1- N-power Agro:

 Wannan tsarin ana bukatar masu shaidar kwalin Diploma, HND da Degree, kuma wanda suka karanci fandin Agric ko Nutrition.

2- N-power Tax

Wannan tsarin suna bukatar masu shaidar kwalin HND da Degree ne kaɗai, Kuma wanda suka karanci fannin Finance, Economic, ko Accounting.

3- N-power Build

Wannan tsarin suna buƙatar masu shaidar karatun SSCE, Diploma, HND da Degree, bugu da kari wanda bashi da takardan shaidar karatu ma zai iya cikewa.

4- N-power Health

Wannan tsarin suna bukatar masu shaidar kwalin Certificate, Diploma, HND da Degree.
Daga cikin wadanda suke bukata akwai:

– Midwives
– Nursing
– Medical Record
– CHO, CHEW, JCHEW
– PHARMACY
– Biology
– Biochemistry
– Health education
– EHO, EVT, EHA

5- N-power Teach

Wannan tsarin suna bukatar masu kwalin NCE, Diploma, HND, da degree.

Kada ku manta ranan Juma’a(26/6/2020) mai zuwa za’a bude wannan Portal din Kuma portal address nasu bai canza ba, wanda
akai amfani da shi na baya shi za’ayi amfani (portal.npower.gov.ng)

Allah Ubangiji Ya bawa kowa sa’a.

Daga Mutawakkil Gambo Doko.
Hausaloaded sun dauko daga shafin Rariya.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button