Zan cigaba daga inda Buhari ya tsaya – Lawan
Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmed Lawan ya ce yana da aniyar ci gaba daga inda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tsaya idan har aka zabe shi a matsayin shugaban Kasar Nijeriya na gaba.
Jaridar Leadership Hausa ta rawaito cewa Lawan, wanda shima ɗan takarar shugabancin ƙasa ne a jam’iyar APC, ya bayyana haka ne a ranar Asabar a lokacin da yake jawabi ga wakilan jam’iyyar APC a zaben fidda gwani na shugaban kasa da za a yi nan gaba a Dutse, jihar Jigawa.
“Duk da cewa gwamnati mai ci ta yi ayyuka da yawa ta fuskar kara habbaka tattalin arziki da samar da tsaro ga ‘yan kasa, amma dai akwai bukatar kara kaimi akan abubuwa da dama.
“Gwamnati ta kashe Kudade masu yawa don habbaka harkar tsaro amma ‘haka ba ta cimma ruwa ba’, ba mu samu nasarar da ake bukata ba, amma hakan ba yana nufin ba mu yi komai ba.
“Kimanin shekaru 23 da na yi a matsayin dan majalisa sun kara min fahimtar hakikanin al’amuran da suka shafi harkokin mulki a kasar nan.” Inji Lawan.
![[Bidiyo] Ni na haɗa auren G-Fresh da Alpha Charles – Jaruma Babiana](https://i0.wp.com/hausaloaded.com/wp-content/uploads/2024/12/Picsart_24-12-25_12-05-31-313-scaled.jpg?resize=220%2C150&ssl=1)





