Kannywood

Jaruma Saratu Gidado Mama Daso ta fito takarar sanata a Kano

A ranar Asabar, 21 ga watan Mayun 2022 ne dattijuwar jaruma, Saratu Gidado, wacce aka fi sani da Daso ta bayyanawa kowa batun fitowarta takara.

Kamar yadda ta sanya a shafinta na Instagram wanda jama’a su ka dinga yi mata fatan alkhairi.

Karkashin fostar ta kara da cewa:

“‘Yan Najeriya barkanmu da safiya da kuma ranar karshen mako.

“Ina mai farin cikin bayyana abinda ke zuciyata na kudirina na tsayawa takara sanata a jihar Kano.

“Nan ba da jimawa ba zan bayyana sunan jam’iyyar da zan tsaya takarar. Amma a halin yanzu ina neman addu’ar ku.”

A can kasa kuma ta sanya cewa burinta shi ne ceto Najeriya daga mawuyacin halin da ta ke ciki.

Wallafar ta dauki hankali kwarai wanda daruruwan mutane su ka dinga yi mata fatan alkhairi tare da nuna farin cikinsu akan wannan ci gaba da aka samu.

Ga ra’ayin mutane da sunka bayyana a shafin nata.

@Young 6658: Kuma wlh dama irinku aka rasa a cikin gwamnati, masu Bude Wuta da balbalin bala’i.

King_andi_2 : Kuma fA zaki iya sabida gaskiya munga aikinki a azumi

Jamilumuhd : Wacce jam’iyya ce?

Saratudaso : @jamilumuuhd Za a sanar bada dadewa ba.

alfirdaus_as_sudais : Kuma abin zaiyi kyau, voice for all, har na hangoki. Allah ya ida nufin alheri

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button