Labarai

An kama ‘yan matan da suka lakada wa kawarsu duka a Yola kan zargin gulma

An kama 'yan matan da suka lakada wa kawarsu duka a Yola kan zargin gulmaRundunar ‘yan sandan jihar Adamawa a arewa maso gabashin Najeriya ta ce ta kama wasu ‘yan mata shida bisa zarginsu da laifin yi wa wata kawarsu “dukan kawo wuka.”

Mai magana da yawun rundunar DSP Suleiman Nguroje wanda ya tabbatar wa da BBC Hausa lamarin, ya ce a yanzu haka ana bincike kafin a gurfanar da su a gaban kuliya.

“Ita yarinyar da aka yi wa dukan tana jinyar raunukan da aka ji mata a yanzu haka, kuma nan da kwanaki kadan za mu tura su kotu don a yi shari’a,” in ji shi.

A makon da ya gabata ne shafin Northern Hibiscuss a Instagram ya wallafa wani bidiyo da ke nuna ‘yan mata sun taru suna jibgar wata budurwa tare da aibata ta da kalamai.

Bidiyon ya jawo ce-ce-ku-ce sosai inda ta kai har aka samu masu rajin kare hakkin dan adam suka shiga maganar tare da kao wa ‘yan sanda rahoto.

Me ya faru a cikin bidiyon?

A bidiyon dai an nuna da farko wata budurwa mai kaya launin shanshanbale na zaune a kan kujera sai wata da ke tsaye sanye da bakaken kaya tana dukan ta kujerar da dorina.

Daga can gefe kuma an ga wasu ‘yan matan suna tsattsaye suna kallon abin da ke faruwa tare da yin surutai.

An jiyo wata daga gefe tana cewa “Fati ya isa haka, ya isa”, amma ga dukkan alamu Fatin wacce ita ce ke dukan ba da niyyar hakura.

Kauce wa Instagram, 1

A bidiyo na biyu kuma sai aka ga lamarin ya koma daki inda wacce ke dukan ke kan gado su kuma masu dukan suka karu har su wajen hudu suna ta jibgarta.

Wata na dukan da dorina wata tana yi da sandar goge-goge wato mop, yayin da wacce ake dukan ke ta tsala ihu kamar rabta zai fita amma ba mataimaki.

Sannan ga dukkan alamu wacce ta dauki bidiyon ma daya ce daga cikin ‘yan matan da ke gidan lokacin da hakan ke faruwa.

Masu dukan dai duk yawanci sun fita hayyacinsu suna ta maganganu na nuna cewa ba sa ko jin nadamar dukan nata.

Short presentational grey line

Laifin me ta yi musu?

A cikin bidiyon dai an jiyo wata daga cikin masu dukan matashiyar tana zaginta tare da cewa “ni da saurayina… da kudinki nake zuwa Abujan ne? Da kudinki nake zuwa Abujan?”

Sai dai hanayniyar masu kara zuga Fati da ta masu ba ta hakuri da ta daina ya hana jin ragowar korafin da Fatin ke yi.

Amma DSP Nguroye ya shaida wa BBC cewa a binciken farko-farko da suka gudanar sun gano cewa ‘yan matan ne suka kira matashiyar gidan da suke daga nan sai suka far mata da duka bisa zarginta da yi musu “wani sharri.”

“To maimakon ko ma mene ne su kawo batun ga ‘yan sanda sai kawai suka dauki doka a hannunsu, wanda hakan bai dace ba.”

“Sun rufe gidan suka taru su biyar zuwashida suka yi mata duka da bulalu a kuma duk irin kukan da take yi ba su kyale ta ba,” cewarsa.

Jami’in ya jara da cewa bayan samun bidiyon ne suka kamo ‘yan matan, “kuma ba su musa mana laifinsu ba sun ce sun aikata.”

Me wacce aka daka ta ce?

BBC ta tuntubi wacce aka yi wa dukan mai suna Sakina Ahmed wacce ta ce kawayen nata ne suka dinga matsa mata cewa ta je su hadu a gidan daya daga cikinsu don a ga sabuwar wayarta.

“Daga baya da suka matsa min sai na ce to mu hadu a gidansu Fati don in duba ta tun da dama ta yi rashin lafiya kuma ta yi korafin ban je duba ta ba.

“Shi kenan muka hada hanya mu wajen hudu muka rankaya muka tafi dukkanmu kawaye har da wata mai aure a cikinmu.

“Da muka shiga gidan aka gaggaisa har muka ci nama, kawai sai daya daga xkinsu ta fara cewa an ce ni na raba ta da saurayinta ya fasa aurenta.

“Sai kawai sauran ma suka fara kawo korafi, wannan ta ce, waccar ma ta ce. Daga nan kawai ba zato ba tsammani sai suka rufe ni da duka.

“Ashe har wasu mutum hudun suka gayyato kawayen yayar Fatin, su takwas haka suka tarar min da mai tsintsiya da mai dorina da mai bel da mai sandan mop,” kamar yadda Sakina ta ce.

Short presentational grey line

Me ya faru bayan nan?

Sakina ta ce bayan sun gama lallasata sai ta lallaba ta tafi gida amma ta kasa gaya wa kowa don sun gargade ta cewa idan ma ta fada za su kara mata fiye da wannan dukan.

“Kuma ba na so maganar ta yadu a duniya don haka sai na yi wa jikina ruwan dumi na kwanta.

“Amma washe gari da safe ciwo ya taso gadan-gadan har na suma sau biyu kuma na dinga amana jini.”

Daga nan ne sai aka garzaya da Sakina asibiti sannan ‘yan uwanta suka kai maganar ga hukuma inda a nane ‘yan sanda suka ce tuni labarin ya je musu.

Har yanzu dai Sakina tana fama da jinyar ciwon da dukan ya saukar mata.

Runudnar ‘yan sanda kuma ta ce za ta hada bayanan asibiti da na binciken da ta tattara don gabatar wa kotu wacce ake sa ran za ta fara sauraron karar ranar 7 ga watan Oktoban nan.

Sai dai BBC ba ta samu jin ta bakin sairan ‘yan matan ba kasancewar suna tsare a hannun hukuma.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button