Labarai

Sojojin Najeriya sun kashe ‘yan Boko Haram/ISWAP 39 a Borno

Advertisment

Aliyu Samba
Sojojin Najeriya sun kashe ‘yan ta’addan Boko Haram/ISWAP kimanin 39 a wani samame da suka kai a arewa maso gabashin jihar Borno.

An kashe ‘yan ta’addan ne a ranar 25 ga Afrilu, a yayin wani aikin share fage na hadin gwiwa da dakarun Operation Hadin Kai tare da hadin gwiwar Civilian Joint Task (CJTF), suka yi a kauyukan Mallum Maja, Gosama da Tesa a karamar hukumar Dikwa.

Wata majiya ta bayyana cewa sojojin sun yi wa ‘yan ta’adda ta’annuti a lokacin da suka far ma maboyarsu, inda suka kashe su da dama a wani samame da suka yi.

Majiyar ta kara da cewa wasu daga cikin ‘yan ta’addan na dauke da bindigogi a lokacin arangamar yayin da wasu kuma aka tarfa su ba tare da makamansu ba.

Wani jami’in CJTF da ya yi magana da harshen Kanuri a cikin wani faifan bidiyo na dakika 2:54 da muka gani ya ce sun kashe 39 daga cikinsu tare da kama AK 47 da 4GT guda 8.

“Har yanzu muna farautarsu a cikin wannan turnuƙu da muke ciki,, muna kauyukansu kuma mun gama da su duka, wannan daya ne daga cikin makamansu da Kwamandan su,” in ji shi.

Wani Jami’in CJTF din daban da ya fito a faifan bidiyon ya ce babu wanda ya taba yin irin wannan a Dikwa, kawo yanzu Boko Haram 39 sun mutu..

Majiyoyi sun ce sabbin hare-haren a karkashin shirin “Operation Lake Sanity” da dakarun Operation Hadin kai da dakarun hadin gwiwa na kasa da kasa (MNJTF) ke aiwatarwa yana samun sakamako mai kyau na dakile ta’addancin Boko Haram/ISWAP.

Advertisment






Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button