Kannywood

[Bidiyo] illolin Fina Finai A Cikin Al Ummah – Daga Bakin Sheikh Ibrahim Aliyu

illolin Fina Finan Hausa A Cikin Al Ummah, Daga Bakin Sheikh Ibrahim Aliyu Kaduna, Malam Yayi Bayani Sosai Game Da Illa Da Matsalolin Da Fina Finan Hausa Suka Jawoma Mutane A Cikin Al’Ummah

Sheikh Ibrahim Aliyu yace yana nan yana rubuta wani rubutu mai taken illolin Fina Finan Hausa,india, Chinese, Nollywood da sauransu malam yace a fina finai aka koyi kidinafin.

Malam yace wani ya kalli fim din wani ya saci yarinya yanzu gashi nan anayi, a fina finai aka koyi fashi da makami a fina finai ana koyi kwacen waya manya manyan laifuffuka a fim aka koya.

A fina finai aka koyi batsa da mace tayiwa namiji kiss a gaban jama’a, a finai finai aka koyi mace tayiwa namiji fitsara, a fina finai mata suka koyi zuwa wurin boka.

A fina finai aka koyi zagin addini da sanya wa mutane raunin addini malam ya kawo misalin cewa a cikin fim ake mutuwa wasa wanda Manzon Allah s.a.w yace babu wasa a cikin mutuwa.

Malam ya fadi abubuwa sosai a cikin wannan bidiyo wanda suke tattare a cikin illa da munin fina finai a cikin al’umma.

Ga Abin Da Malam Yake Cewa Game Da Fina Finan Hausa

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button