Labarai

Ba ni ƙaunar ‘yan ta’adda – Sheikh Gummi

Advertisment

Ba ni ƙaunar ‘yan ta’adda – Sheikh Gumi
Ba ni ƙaunar ‘yan ta’adda – Sheikh Gumi

Sanannen malamin addinin musulunci a Nijeriya Sheikh Ahmad Gumi, ya ce ba ya ƙaunar ‘yan ta’adda ko alama.
DCL Hausa ta ba da labarin cewa Gumi na magana ne a lokacin da yake martani ga kalaman mai magana da yawun shugaban ƙasa Femi Adesina.
Punch ta ba da labarin cewa a wani dogon rubutu da Adesina ya yi, mai taken “Ina farincikin wannan aiki. Kai fa? A cikin rubutun yana yabon ayyukan da jami’an soji ke gudanarwa na kakkabe ‘yan ta’adda a arewacin Nijeriya.
Sai dai wasu rahotanni sun bayyana cewa Sheikh Gumi ba ya jin dadin irin hare-haren da ake kai wa ‘yan bindigar.
A cikin rubutun Adesina, bai ambaci sunan Sheikh Gumi ba, amma dai ya ce duk mai son ayyukan ta’addanci, shi ne zai ji ba dadi a ayyukan sojoji kan ƴan bindiga.
A nasa martani, a wani rubutu da ya yi mai taken “Yaki ba zai taba zama hanyar lalama ba a kodayaushe a kuma ko ina” Gumi ya barranta kansa da cewa yana kaunar ayyukan da ‘yan bindiga ke aiwatarwa.
Yace wadanda ke kiransa da masoyim ƴan bindiga, to ba haka bane, yace shi masoyim Nijeriya ne da yankinsa da jiharsa da al’ummar sa.

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button