Labarai

Kotu ta aike da matasa 2 gidan yari bisa yin bahaya a cikin masallaci a Kaduna

A yau Alhamis ne wata kotun shari’a da ke zamanta a Magajin Gari a Jihar Kaduna, ta bayar da umarnin a ci gaba da tsare Nura Usman da Adamu Dauda a gidan gyaran hali bisa zargin yin bahaya a cikin masallaci.

Rundunar ƴan sanda ce ta gurfanar da Usman da Dauda da laifin samun al’umma da kokarin haifar da tarzoma.

Alkalin kotun, Rilwanu Kyaudai, ya ɗage sauraron ƙarar zuwa ranar 28 ga watan Afrilu domin ƴan sanda su gabatar da shaidu.

Tun da fari, Lauyan masu shigar da kara, Ibrahim Shuaibu, ya ce wasu al’umma sun mika Usman da Dauda ga ofishin ƴan sanda na Tudun Wada a ranar 11 ga Afrilu.

Ya ce an kama Usman ne yana yin bahaya a wani masallaci da ke kan titin Alkalawa, Tudun Wada Kaduna da misalin karfe biyu na rana.

Ya ce Dauda, ​​wanda ake kara na biyu ya yi alkawarin bai wa Usman N20,000 domin ya yi bayan gida a masallaci.

Sai dai kuma duk su biyun sun musanta aikata laifin.

~ Daily Nigerian hausa

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button