Addini

Muna Yabawa Shugaban Kasa Bisa Bude Rumbunan Abinci Saboda Azumi —Sheikh Bala Lau

A sati biyu zuwa ukku da na wuce kungiyar izzalatul bidi’ah wa’ikamatus sunnah sun bude sabon masallaci a garin abuja inda kuma shugaban kasa Muhammadu Buhari ya samu halarta bude masallacin a nan ne shugaban kungiyar Sheikh Abdullahi bala lau yayi kira ga Muhammadu Buhari da ya taimaka a bude rumbun abinci saboda tausayawa talakawa.

To shine shekaranjiya buhari ya bada umurnin bude rumbin abinci tare da tan 40,000 na hatsi shine sheikh Abdullahi bala lau yayi murna kamar yadda shafin jibwis Nigeria sunka wallafa a shafinsu.

A yayin da ake cikin wata mai alfarma na Ramadan, shugaban kasar Nijeriya Muhammadu Buhari ya bada umurnin bude runbun abinci na gwamnatin tarayya, tare da fatar da tan 40,000 na hatsi saboda saukakawa al’umma a cikin wata mai alfarma. Wannan yana kunshe ne a cikin wata sanarwa da ma’aikatar noma, kiwo da raya karkara ta fitar a jiya talata.

Lura da wannan, shugaban kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa Iqamatis Sunnah, Ash-Sheikh Abdullahi Bala Lau ya jinjinawa shugaban kasan bisa wannan mataki da ya dauka, wanda a cewar sa zai kawo sauki matuka ga al’umma.

Idan ba a manta ba dai, a watan da ta gabata, Sheikh Bala Lau yayi kira na musamman ga shugaban kasa da ya bude rumbunan abinci da asusun gwamnati saboda tallafawa al’umma a cikin watan Ramadaan. Sheikh Lau yayi wannan kira ne a lokacin da shugaban kasan ya halarci bude babban masallaci da kungiyar IZALA ta gina a Abuja.

“Alhamdulillah, muna jinjina ga shugaban kasa, wannan ba karamin taimakawa talakawa zai yi ba. Kuma muna kira ga hukumomin da alhakin raba wannan kaya ya shafa su hada kai da shugabannin al’umma da suka fi kusa da su kamar malamai da sarakuna wajen raba wannan tagomashi don ganin cewa wannan tallafi ya isa zuwa ga talakawa.” Inji Sheikh Bala Lau.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button