Addini

Ramadaniyyat: 1443 [11]Tsakanin Ibada Da Al’ada – Dr Muhammad Sani Umar R/lemo

Advertisment

1. Duk wani tasaruffi na ɗan’adam a maganganunsa da ayyukansu bai wuce iri biyu ba:

Na ɗaya, Ibadu, waɗanda su ne addininsa.

Na biyu, al’adu, waɗanda su ne gudanar da mu’amalolin rayuwarsa ta yau da kullum.

2. Binciken ƙwaƙwaf a cikin ƙa’idoji na shari’ar Muslunci ya tabbatar da cewa, duk wata ibada ba za ta tabbata ba sai ta hanyar shari’a kaɗai.

Advertisment

3. Amma al’adu na rayuwar mutane ta yau da kullum, shari’a ta nuna cewa, babu abin da ake haramta musu daga ciki sai abin da Allah shi da kansa ya haramta.

4. Domin umarni da hani su ne shari’ar Allah. Ibada kuwa dole ne ta zamanto abin da aka yi umarni da aikta shi. Duk abin da bai tabbata ba ta hanyar umarnin Allah da Manzonsa, to ta yaya zai zama shari’ar Allah?

5. Hakanan duk wata al’ada da shari’a ba ta yi hani a kanta ba, to ba za a yi mata hukunci da haramun ba.

6. Saboda haka ne Imamu Ahmad da sauran malaman hadisi suke cewa: ƙa’ida dangane da ibada ita ce, sai an samu nassi daga Allah ko Manzonsa. Ba za a ɗauki wani abu a matsayin addini ba har sai da izinin Allah, idan kuwa ba haka ba, to za mu shiga ƙarƙashin faɗar Allah: (Ko dai suna da wasu abokan tarayya ne da suka shar’anta musu wani abu na addini wanda Allah bai yi izinin yin sa ba?..) [Shura, aya ta 21].

7. Hakanan kuma ƙa’ida game da al’adu ita ce, an yi afuwa da rangwame, ba za a haramta wata al’ada ba sai wadda Allah (SAW) da kansa ya haramta. Idan kuwa ba haka ba, to za mu shiga ƙarƙashin faɗar Allah: (Ka ce (da su): “Ku ba ni labarin abin da Allah Ya saukar muku na arziki, sannan kuka mayar da wani haram wani kuma halal”..) [Yunus, aya ta 59].
[Duba, Ibn Taimiyya, Majmu’ul Fatawa, juzu’i na 29, Shafi na 16-17].

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisment
Back to top button