Labarai

Yadda na dinga lalata da ɗan ciki na duk don in haifa wa sabon miji na da, Wata mata

Wata mata ta fallasa yadda ta dau tsawon lokaci tana lalata da dan cikin ta, don kawai ta haifa wa mijin da, LIB ta ruwaito.
Matina Agawuawua, mai zama a Yelwata cikin jihar Nasarawa, ta rasa mijin ta na farko ga harin makiyaya a arewancin Najeriya. Bayan ta haifi namiji a auren ta na fari.
Ta sake wani auren, bayan shekaru da mutuwar mijinta, sai dai, ta fuskanci matsalar rashin haihuwa da mijin nata na biyu, Mr James.
Bayan shekaru shida da aure ba haihuwa, Matina ta fara fuskantar tsangwama daga mahaifiyar mijin ta da mijin nata, ta hanyar yi mata barazana akan ko dai ta haihu ko kuma a raba auren kamar yadda labarunhausa ta fakaito
Mijin Matina yayi barazanar kara aure, wanda hakan ya jefa ta a matsananciyar damuwa, saboda yadda ita da mijin nata suka hada kudi suka gina gidan da suke ciki, kuma kason ta yafi yawa.Yadda na dinga lalata da dan ciki na duk don in haifa wa sabon miji na da, Wata mata
Matina ta shiga damuwa ganin yadda ake kokarin kawo wata mata a gidan da ita da mijin ta suka gina.
A dalilin haka ne, Matina ta yanke shawarar yin lalata da yaron ta mai kananun shekaru, wanda ta haifa a aurenta na farko, don ganin idan zata iya haifa wa mijin ta da.
Munyi aure sama da shekaru shida, amma bamu sami haihuwa ba, saboda matsalar daga mijina take, kamar yadda rahoton likita ya nuna, sannan na ji jita-jita akan yadda ya ke shirin kara aure, saboda na gaza haifa mishi da,” Matina ta bayyana wa The Nation.
Matina ta bayyana wa manema labarai yadda tayi gwaji da kanta, tunda mijin nata yaki gwadawa, inda sakamakon ya nuna babu abunda ke da mun ta a lafiyan ce.
Don tabbatar da ita ba juya ba ce, ta yanke shawarar yaudarar dan da ta haifa, dalibi a Akwanga, don yin lalata, tare da jan kunnen shi da ya bar hakan a matsayin sirri.
Ta bayyana wa The Nation cewa:
“Tunda yaki yarda mu je asibitin a duba mu, yana cewa babu abunda ke damun shi, na yanke shawarar fahimtar da dan yarona, wanda ke da shekaru 16 kacal, kuma yake karatu a Akwanga.
“Ina kai masa ziyara akai-akai. Yana zama ne a wani gida tare da ‘yan uwana, inda nake zuwa wani lokacin wurin su, musamman a karshen sati da bana zuwa kasuwa.
“Maganar gaskiya nasha wahalar soyayya da dan da na haifa, amma halin da nake ciki ne ya tilasta ni. Ina bukatar tabbatar da idan zan iya haihuwa.
“Nasan miji na kwarai. Idan ya fahimci ina lalata da wani mutum a waje, halaka ni zaiyi.
“Yawancin lokaci ina kokarin ziyartar da na a Akwanga, idan na gama al’ada. Na yanke shawarar fara kaunar sa, tare da jawoshi jikina. Mun samu kusanci matuka, hakan yayi sanadiyyar fara lalatar mu.
“Wata rana na kai mishi ziyara bayan na gama al’adata. Misalin karfe 11:00 na dare. Na rike hannun shi tare da zama kusa dashi.”
Bayan yin lalata da dan ta a watan Janairun 2022, bata ga al’adarta ba, yayin da gwajin da tayi ya tabbatar mata da tana dauke da juna biyu.
Sai dai, bayan ta sanar wa mijinta, ya zarge ta da raina mishi hankali. Inda ya tuna ma ta cewa, sun dauki tsawon watanni uku ba tare da sun sadu da juna b, sannan ya musanta yi ma ta cikin.
Mr James ya zargi Matina da aikata zina, sannan ya yi barazanar halaka ta, hakan yasa ta fallasa yadda tayi lalata da dan ta.
An tuhumi dan Matina, inda ya tabbatar da yin lalata da mahaifiyarsa.
Matina ta bayyana wa manema labarai cewa:
“Ni ba sakaryar mace bace. Kawai ni mace ce wacce ke kaunar mijin ta matuka, kuma bana son bata mishi rai ko rasa shi.
“Na yi hakan ne don tseratar da aure na. Saboda yadda na samu labarin yana son kara aure, bisa shawarar da iyayen shi suka ba shi na cewa matar sa ta biyu zata zauna a dayan sashin da muka sha wahalar ginawa tare.
“Na yi hakan ne don haifa mishi da, da kuma dakatar da shi daga Kara aure. Karin auren shi alama ce ta kora ta daga gidan, hakan zai sa in rasa abunda muka sha wahalar tarawa tare.
“Dubi shekaru na. Kullum tsufa nake, amma miji na bai shirya magance matsalar ta hanyar neman lafiyar sa ba.”
Mijin Matina ya tsaya akan bakar sa na kin amincewa da cikin da ba nashi ba.
Hakan yasa ta ji tsoron mijin nata zai iya halaka ta, inda ta bar gidan.
Sai dai, ta ce tana da niyyar neman lauyan da zai tsaya ma ta akan gidan, tunda tana da kaso mafi yawa wajen gina gidan.
Kamar yadda tace:
“Ba zan zubar da cikin ba. Sai dai, zan bari in haife shi. Saboda na dade ina neman haihuwa tsawon lokaci, ba zan bar shi ya tafi haka nan ba. Cikin da na ne.
“Yanzu mutumin yana barazanar halaka yaro na saboda ya dirkamin ciki, dole in fitar da dana daga Akwanga, in kaishi wani wuri don tseratar da rayuwarsa.
“Dalili shine, saboda ni ce na saka shi cikin wannan sarkakiyar. Dole kuwa in kare shi.”
Mijin yayi alawadai da halayyar matarsa, har ya kada baki yace:
“Ta yaya zata bar dan ta ya dirka mata ciki, sannan ta yi kokari makala min? Ya zata yi haka? Hakan ya fusata ni kwarai.
“Amma idan ta shirya tafiya, ta tafi mana. Tare muka gina gidan, duk abunda take so, ba ni da matsala da hakan.”

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button