Labarai
Zarar Bunu: Ganduje Ya Dakatar Da Salihu Tanko Yakasai Sakamakon Sukar Gwamnatin Buhari
Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya dakatar da mai taimaka masa na musamman a kan kafafen yaɗa labarai Salihu Tanko Yakasai, sakamakon sukar gwamnatin Shugaba Buhari, in da ya bayyana gwamnatin a matsayin wacce ba ta tausayin ‘yan Najeriya.
Sanarwar dakatarwar na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Kwamishinan yaɗa labarai na jihar Kano, Malam Muhammad Garba ya sanyawa hannu.
Sanarwar ta ƙara da cewa a matsayin Salihu Tanko Yakasai mai riƙe da muƙamin gwamnati abu ne mai wahala a banbance tsakanin ra’ayinsa da kuma ra’ayin gwamnati.
Haka kuma sanarwar ta ce matakin dakatarwar ya fara nan take.