Labarai

Shin Kun San Laifin Malam A Gurinsu ? Karanta ~ Datti Assalafy

Advertisment

Wanda ya kafa jaridar Sahara Reporters sunansa Omoyele Sowore, ya kafa jaridar ne a Kasar waje, ‘dan kabilar yarbawa ne, bayarbe ne, babban ofishin jaridar yana Lagos, yarbawa ne suke gudanar da jaridar sai wasu gurbatattu a cikin hausawa da suke tayasu aiki

A wani bincike da na gabatar, da zuwan Malam Dr Isah Ali Ibrahim Pantami ma’aikatar sadarwa ya karba ne daga hannun tsohon Minista bayarbe, Malam yazo ya tarar da abubuwa na rashin gaskiya da mamaya wanda kabilar yarbawa sukayi a ma’aikatar sadarwa, sai Malam ya rushe kabilancin da sukayi ya kawo adalci da gyara mai ma’ana

Wannan abinda Malam yayi ya taba zukatan yarbawa, sai suke amfani da jaridar Sahara Reporters na ‘dan uwansu bayarbe suke ta kokarin yiwa Malam batanci da sharri don su goga masa kashin kaji da bakin jini don su huce takaici

Don haka jama’a ku gane kuma ku fahimta, cin mutuncin Malam da ake a jaridar yarbawa ta Sahara Reporters kabilanci ne, kuma laifinsa kenan ya wargaza shirin mamaya da yarbawa sukayi a ma’aikatar sadarwa, shiyasa zakuga Sahara Reporters babu ruwansu da yiwa sauran ministoci batanci da sharrin sai mininstan Sadarwa Dr Isah Ali Ibrahim Pantami  kadai

Don haka ina kira ga ‘yan uwa ‘yan Arewa, mu tashi tsaye mu kare daraja da martaban Malam Isah Ali Ibrahim Pantami kafin tsinannun mutane masharranta su Sowore su sami galaba a kanshi, don Wallahi mutanen nan idan sun samu sa’a a kan Malam zasu kawar dashi, domin abinda sukayi yanzu sun taimaki ‘yan Boko Haram ne wajen nuna makwancin Malam

Sannan abinda Sowore yake mana bayan kabilanci to akwai kiyayya da gaba na banbancin addini, yana fada da addinin Musulunci ne, Insha Allahu sai Sowore ya wulakanta kafin Allah Ya tabar dashi, Insha Allahu duk wani abu marar daraja a Nigeria sai yafi Sowore daraja da taimakon Allah, zamu hana idon mu bacci mu kai karansa gurin Allah Madaukakin Sarki

Kuma kwangila ake bashi, kudi makudai yake samun a dalilin wannan batanci da yake yiwa ‘yan Arewa da Musulunci, shine wanda watannin baya ya kira taron juyin juya hali a Nigeria wanda daga karshe DSS suka kamashi, makiyin Nigeria da zaman lafiya wanda yake neman hanyar kunna wutar rikici da fitina a cikin kasa

Yaa Allah Ka kaskantar da Sowore
Yaa Allah Ka wulakanta Sowore
Yaa Allah Ka watsa al’amarin Sowore
Yaa Allah Ka nuna mana karshensa yana wulakantacce
Yaa Allah Ka kare mana Malam Isah Ali Pantami, Ka kunyata makiyansa, Ka bashi nasara akan mutanen banza Amin

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button