Labarai

Abin Da Ke Kai Ni Wurin Dan Bindiga Yana Zina Da Ni Matar Aure

Advertisment

Abin Da Ke Kai Ni Wurin Dan Bindiga Yana Zina Da Ni Matar Aure
Abin Da Ke Kai Ni Wurin Dan Bindiga Yana Zina Da Ni Matar Aure

Wata matar aure da ke zuwa wajen wani dan bindiga yana lalata da ita ta ce gudun kada a kashe iyayenta ne ya sa ta ba shi kanta.Matar da ke zaune a kauyen Tankarau a yankin Madaci da ke Karamar Hukumar Zariya ta Jihar Kaduna ta bayyana sunan dan fashin bindigar da take zuwa wurinshi yana lalata da ita, inda ta faɗi sunansa Idi Dan Ibrahim.
Aminiya ta ruwaito Matar ta bayyana hakan ne a lokacin data shiga hannu.
IndaTa ce; “Tun da nake zuwa wajen dan bindigar ya yi lalata dani sau daya ya taba ba ni N5,000 daga baya idan na je, ba na yarda da shi,sai dai ince mishi ba ni da lafiya ko ina jini, don haka sai ya daina ba ni komai.”
Ta ce bayan kama ta ta shiga damuwa saboda mijinta da ’ya’yanta duk sun shiga damuwa saboda ganin halin da ta shiga.

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisment
Back to top button