Labarai
Matashin da ke sace wayoyin fitilun kan titi a Kano ya shiga hannu
Dubun wani matashi dake yanke wayoyin futilun kan titi a Jihar Kano, mai suna Umar Abdullahi ta cika inda ya shiga hannun rundunar tsaro ta Civil Defence.
Da ya ke jawabi a shelkwatar rundunar da ke Kano, matashin ya shaida da cewa wanann ne karo na biyu da ya ke yanke wayoyin kuma a wancan kokaci ya sayar da wayoyin akan kuɗi Naira dubu 150.
Abdullahi ya ce hakika ya yi nadama akan wanann laifi da ya aikata, sai dai yace ba zai sake aikatawa ba.
Kakakin rundunar ssaro ta Civil Defence na Jihar, Ibrahim Idris Abdullahi ya ce jami’an su sun samu nasarar kama matashin a yankin unguwar Hotoro NNPC, inda ya ce tuni suka fara cigaba da fadada bincike domin kamo sauran wadanda ake zargi
Ya kara da cewa za su gurfanar da shi a gaban kotu.