Yanzu – Yanzu : Yan Boko Haram sun sace akalla matafiya 35 a hanyar Damaturu zuwa Maiduguri
Kamar Yadda Daily Nigerian na ruwaito, cewa ‘yan ta’adda suka kai hari a dogon jerin gwanon masu hawa a kusa da Garin Kuturu a Jakana, a Damaturu-Maiduguri hanya a ranar Jumma’a 5:00 pm
Maharan sun kashe wata mata a cikin motar Borno Express, wadanda suka kona akalla motoci bakwai a wurin da aka kai harin.
Bayanai sun ce maharan, wadanda suka bayyana a cikin kakin soji, sun sanya shingen kan hanya a kan babbar hanyar da motocin Hilux guda biyar kafin su sace fasinjojin.
“Fasinjojin sun fara ganin wuta mai ci, amma sun yi zaton wutar daji ce, ba tare da sanin cewa tuni suka yi wa wani direban motar Dangote kwantan bauna suka cinna masa wuta ba,” in ji wata majiyar tsaro da ta gwammace a sakaya sunan ta.
“Amma yayin da suke zuwa wurin, sai suka hangi maharan sun nufo su kan manyan motoci dauke da manyan makamai, Kafin su juya motocinsu su gudu, maharan sun riga sun cim masu.
“Da yawa daga cikin fasinjojin sun gudu zuwa daji, an sace 35, motoci masu zaman kansu biyu da babbar mota guda an banka musu wuta. Motoci tara na fasinjojin da aka sace ma an bar su a wurin yayin da aka wawushe kayayyakinsu, ”in ji majiyar.