Labarai

Ana yaudarar magoya baya suna mutuwa wajan bidi’a amma ace sun yi shahada – Dr. Idris Bauchi

Advertisment

Al’amarin da ya faru a jihar Kaduna daren Lahadi wanda anka sakawa mutane bomb a wajen taron mauludi wanda tabbas yayi asarar rayuwan mutane sama da 100.

Wanda dukan musulmi yayi Allah wadai da abinda wannan jami’an tsaro sunka aikata shine a wajen karatu shi dr abdulaziz dutsen tashe yayi magana akai a cikin wani faifan bidiyo da wani shafin tiktok mai suna @babayoabdullahi sunka wallafa inda yake cewa.

“Taron mauludi suke fa a shekarar jiya ranar lahadi jirgi yazo, bayin Allah nan yayi musu ruwan bama bamai bayan sunzo kwashe yan uwansu ya sake dawowa, wallahi duk wanda yace muku ga adadin da anka kashe yayi muku karya ne, wasu suce dari 100 wasu ma ƙonewa sunkayi ba’a ga gawar su ba.

To kunsan babban Sherrin shine nake so in fada yaudar magoya baya da ake yi mutum ya mutu wajen bidi’a ace yayi shahada, wallahi tallahi abinda yan shi’a su al-zazzkay sukeyiwa magoya bayansu kenan su dauke su, suje abuja da su suje wajen zanga-zanga ace yayi shahada .

Domin a kafafawa na baya gwiwa suma suje a kashe su irin wannan, to kaga abinda yake faruwa kaga wannan wajen mauludi ne, bidi’a ne, wannan taron na bidi’a ne kuma taro ne mata da maza, taron da ya saɓawa Allah ,taron da Allah yake fushi da shi, an kashe su ana yaudarar su ana cewa wai shahada ma sukayi.

Ga wannan sharri malamai kuji tsoron Allah musamman malaman bidi’a dilallan sharri wallahi zaku hadu da Allah, mauludi ba addini bane a ranar da anka haifi manzon Allah baiyi ba, kuma baice ayi ba- injj dr. Idris.

Ga bidiyon nan.

@babayoabdullahi♬ original sound – malam

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button