Labarai

Ƴan bindiga sun kashe mutane 38, inda su ka ƙona motoci da kayan abinci a Kaduna

Ƴan bindiga sun kashe mutane 38, inda su ka ƙona motoci da kayan abinci a Kaduna
Gwamnatin Jihar Kaduna ta baiyana cewa ƴan bindiga sun kashe mutane 38 a hare-haren da su ka kai a ƙauyukan Ƙaramar Hukumar Giwa.
Da fari dai, jami’an tsaro na sojoji da yan sanda ne su ka bada rahoton cewa mutane 20 sun rasa rayukansu a harin da ƴan ta’addan su kai Giwa.
Haka-zalika Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na Kaduna, Samuel Aruwan a wata sanarwa da ya fitar ya ce ƴan bindigan sun kai hari a ƙauyukan Kauran Fawa, Marke da Riheya a garin da ke Giwa inda su ka kashe mutane 20.
Ya ƙara da cewa motoci manya da kanana, gami da kayan amfanin gona su ma an ƙona su.
“Gwamna Nasiru El-Rufai ya yi baƙin ciki game da harin, inda ya yiwa iyalan waɗanda abin ya shafa ta’aziya,” in ji Aruwan.
Sai dai kuma rahotannin da su ke fitowa yanzu sun baiyana cewa adadin mutanen da su ka rasa rayukansu a harin ya kai 38.
Aruwan ne ya tabbatarwa jaridar DAILY NIGERIAN a yau Lahadi.
“Bayan rahoton cewa ƴan ta’adda sun hallaka mutane 20 a karamar hukumar Giwa, Jami’an tsaro sun tabbatarwa gwamnatin Kaduna cewa adadin mutanen da a ka kashe ya ƙaru zuwa 38,” in ji Aruwan.
“An gano sunayen 29 da ga ciki, in da 9 kuma ba a kai ga gano sunayen su ba,”
Ga sunayen waɗanda su ka rasa rayukansu a harin:
1. Rabi`u Wada
2. Salisu Boka
3. Alh Nura Nuhu
4. Alh Bashari Sabiu
5 Alh Lawal Dahiru
6. Abbas Saidu
7 Inusa Kano
8 Malam Lawal Nagargari
9. Malam Aminu
10. Lawal Maigyad
11. Alh Mustapha
12 Lawal Aliyu
13 Sale Makeri
14 Sani Lawal
15 Auwal Umar
16 Jamilu Hassan
17 Badamasi Mukhtar
18 Malam Jibril
19 Lawal Tsawa
20 Sule Hamisu
21 Sadi Bala
22 Kabiru Gesha
23 Abubakar Sanusi
24 Saiph Alh Abdu
25 Haruna Musa
26 Lawal Hudu
27 Malam Shuaibu Habibu
28 Malam Yahaya Habibu
29 Abubakar Yusuf.Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button