Labarai

Asirin Wani Mutun Ya Tonu Bayan Ya Daɗe Yana Kaiwa Ƴan Bindiga Bayanan Sirri A Jihar Katsina

Kamar yadda matsalar tsaro ke addatar arewa maso yamma yanzu nan mun samu wani rahoto daga wani mutum mai suna cmr Nura siniya ya kawo mana wannan rahoto.

Kamar yadda kuke gani Shugaban ƙaramar hukumar Jibia ne Hon. Bashir Sabi’u Maitan, ya kama wani mutum da hannun shi mai suna Aminu Gangara da ya shahara wajen bada bayanan sirri ga ƴan bindiga (Informer) wanda ake zargin yana da hannu dumu-dumu a ta’addancin da ake a garin Bugaje da Gangara da kuma garuruwan da suke ƙarƙashin Masarautar Ɗaɗɗara dake Jibia a jihar Katsina

Asirin Wani Mutun Ya Tonu Bayan Ya Daɗe Yana Kaiwa Ƴan Bindiga Bayanan Sirri A  Jihar Katsina

A rahoton da muka samu an zargi Aminu Gangara da kaiwa ƴan bindiga bayanan sirri akan wani Attajirin yankin da barayin dajin suka ɗauka Alhaji Tasiu Waliyi da sauran wasu mutane a yankin.

Muna roƙon Allah ya ƙara tona asirin duk wani mai hannu a cikin taɓarɓarewar rashin tsaron da ya addabi yankin mu na Arewa da Najeriya baki ɗaya.”Asirin Wani Mutun Ya Tonu Bayan Ya Daɗe Yana Kaiwa Ƴan Bindiga Bayanan Sirri A  Jihar Katsina

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button