Ganduje ya ce a shirye yake ya sa hannu a hukuncin kisa kan mawakin Da Ya zagi Annabi
Gwamnan jihar Kano a Najeriya Abdullahi Umar Ganduje ya ce a shirye yake ya sanya hannu kan hukuncin kisan da wata Babbar Kotun Musulunci ta yi wa Yahaya Shariff Aminu, sakamakon samun sa da laifin ɓatanci ga Manzon Allah SAW, idan bai ɗaukaka kara ba.
Gwamna Ganduje ya ayyana haka ne a yayin wata ganawa da malamai da kungiyar Lauyoyi ta Kano da kungiyar lauyoyi Musulmi, da shugabannin hukumomin tsaro da ke jihar a yammacin yau Alhamis a Africa House da ke fadar Gwamnatin Kano.
Tun a watan Maris na 2020 Aminu Sharif, mazaunin unguwar Sharifai da ke ƙwaryar birnin Kano ya yi wata waƙa, wadda ya yi ɓatancin a cikinta.
Gwamna Ganduje ya ce biyo bayan yadda al’ummar jihar da malamai ke ta matsin lamba kan ganin ya sa hannun a kan takardar hukuncin ya sa ya bayyana matsayinsa, amma ya ce tun da kotu ta bai wa Yahya Shariff kwana 30 dole sai a jira har sai wa’adin ya cika.
Haka zalika Gwamna Ganduje ya ce akwai bukatar malamai su ci gaba da wayar da kan al’umma don gudun samun rikici tsakanin ƙungiyoyin addini da ake da su a jihar.
Su ma dai ƙungiyar lauyoyi sun yi na’am da wannan mataki da gwamnan na Kano ya dauka, inda suka ce ya kamata al’umma su fahimci abun da doka ta ce kafin su yanke hukunci.
Bbchausa na ruwaito,a ranar 10 ga watan Agustan da muke ciki ne wata Kotun Shari’ar Musulunci da ke zamanta a filin Hockey da ke Titin Gidan Zoo ta yanke wa Yahaya Shariff hukuncin kisan bayan ya amsa laifinsa.