Labarai

Babbar Kotun Tarayya Da Ke Abuja Ta Ki Bada Belin Abba Kyari

Advertisment

Wata Babbar kotun Tarayya a Abuja taki amincewa da bukatar beli da tsohon kwamandan rundunar Aiki Da cikawa ta IRT, DCP Abba Kyari ya nemi kotun ta bashi.kamar yadda voahausa na ruwaito"Ina fama da hawan jini da ciwon siga", in ji Abba Kyari yayin da ya ke ɗaure a hannun NDLEA
Lauyoyin Abba kyarin tun farko sun shaidawa kotun cewa, wanda suke karewa yana fama da matsanancin ciwon sugar da kuma hawan jini
Don haka bisa la’akari da wannan su ka nemi kotun ta amince da bukatar neman belinsa.
Sai dai lauyoyin hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyi ta Najeriya wato NDLEA sun yi adawa da bukatar inda suka nuna fargabar wanda ake karar ka iya yin katsalandan da shaidu.
Tun farko dai hukumar ta NDLEA ta nemi kotun data bata damar tsare Abba karin na makonni biyu don zurfafa bincike.
Da yake yanke hukunci akan batun, Mai Shari’a Eyang Ekwo yayi watsi da bukatar belin, maimakon haka ya nemi a rika bashi cikakken kulawa da lafiyarsa a inda ake tsare dashi.
Kotun ta sanya ranar goma sha biyar ga watan maris za a dawo don ci gaba da sauraron shari’ar.

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisment
Back to top button