Yan Jarida Sun Fara korafi Akan Cin Mutuncin Da Ankayi Musu Akan Labarina Episode 11
A cikin shirin labarina season 3 episode 11 zango na ukku kashi na 11 Wanda anka nuna irin yadda dan jarida yazo daukar rahoto wajen sarkin waka wanda anka ga sun nuna anci mutuncin aikinsu wanda wani matashi a shafin facebook mai suna abdulsamad Ishaq yayi korafi ga abinda yake cewa.
“Wannan AI Cin Mutunci ne!
Ga duk wadanda ya Kalli shirin labarina series na Daren jiya zai fahimci gaskiyar abinda nake nufi.
Babu shakka Aminu Saira ya kware wajen bada umarni a fina finai daban daban na kasar HAUSA.
Naga idan zakuyi film, Wanda ya shafi likitoci, ko Yan sanda, zuwa kuke ku koyi yadda suke aikinsu.
Sannan kuyi acting akansa, meyasa sai aikin jarida zakuyiwa yadda kukeso.
A gaskiya Mallam saira, ba haka ake ba, wannan cin mutunci ne da cin fuska, Kuma Wanda kuka bawa character na acting a matsayin Dan jarida ma, ba haka ake ba.
Kuma duk abinda dukkanin ku a Kannywood kuka zama a yau, Yan jarida ne, suka baku gudummawar, har kuka shahara haka.
Kai Kuma SarkinWakawai har da fadin a bada kudin MOTA.
To ka nutsu Dan jarida, wakilin al’umma ne, Kuma jakada ne ba mabaraci ba.
Kamar yadda ake cin mutuncin ku, ake zaginku, kuke fitowa ku bayyana bacin ranku, to muma haka abin yake.
Duk da dai Dan jarida yafi Dan film, da mawaki, kima da daraja a idon mutane.
Da yawa daga cikin ku, jarida ce silar daukakarku.
HABA DA ALLAH
ABDUSSAMAD ISHAQ
11-09-2021.”
Shima wani matashi gen sunusi yayi martani kamar haka.
“Shin a gaske ma haka Celebrities suke yiwa ƴan Jarida idan sunzo Interview dasu a ƙarshe sai Celebrityn yace a nema musu kuɗin Mota su koma office?
Cc: Zainab Ishaq Nadiya Ibrahim Fagge Basheer Sharfadi Aliyu Sufyan Alhassan”