Kannywood

Gwamnan Alfawa kwana Casa’in ya zamo Gwarzon Jarumi ‘Best Actor’ A 2021

Ado Ahmad Gidan Dabino ya zama gwarzon jarumi na shekarar 2021

Fitaccen jarumi kuma Furodusa a masana’antar finafinai ta Kannywood Ado Ahmad Gidan Dabino M O N, wanda aka fi sani da Malam Adamu Ko Gwamnan Alfawa a cikin shirin Kwana Casa’in, ya zama gwarzon jarumi na shekarar 2021 a taron fitar da gwarzon jarumi na Africa wato Wamma Award 2021, wanda aka gudanar a Jamhuriyyar Nijar.
Taron wanda aka gudanar da shi a daren jiya asabar a Palais Des Cogres Niamey ya samu halartar jarumai daga kasashe da dama na Africa,jaridar dimokuradiyya na tattara labarin.
Jarumin ya samu wannan gambun ne bisa kokarin da ya nuna a cikin shirin Kwana Casa’in, wanda hakan ta ba shi damar doke sauran jaruman da suka shiga gasar da shi wanda ya ba shi sa’ar maza fitaccen jarumi na shekarar 2021.

Ado Ahmad Gidan Dabino ya zama gwarzon jarumi na shekarar 2021
Ado Ahmad Gidan Dabino

Ko da ya ke ba wannan ba ne karo na farko da farumin ya fara lashe gasar Gwarzon jarumi, domin a shekarun baya ya taba lashe Kambun gwarzon jarumi da fim din Juyin Sarauta. Amma ko da muka yi magana ta sha Ado Ahmad Gidan Dabino din ta waya. Ya bayyana farin ciki sa da lashe wannan gasa, domin a cewar sa hakan ta ba shi kwarin gwiwa nan gaba sai iya zama gwarzon duniya tun a yanzu ya samu zama gwarzon jarumai na Africa.
Ado Ahmad Gidan Dabino ya zama gwarzon jarumi na shekarar 2021
Ado Ahmad Gidan Dabino ya zama gwarzon jarumi na shekarar 2021

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button