Labarai

Sai dai Buni ya dawo a matsayin gwamna amma ba shugaban APC ba — El-Rufai

Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya ce sai dai Mai Mala Buni ya dawo a matsayin gwamnan Jihar Yobe, amma ba a matsayin shugaban riƙo na jam’iyar APC ba.
El-Rufai ya fadi hakan ne a wata hira da ya yi a shirin ‘Politics Today’ a tashar Channels TV a jiya Laraba.Sai dai Buni ya dawo a matsayin gwamna amma ba shugaban APC ba -- El-Rufai
A cewar El-Rufai, Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari na da cikakken goyon baya ga Gwamnan Jihar Naija, Abubakar Sani Bello kan ya karbi ragamar riƙe jam’iyar.
Ya kuma zargi Buni da yin maƙarƙashiya don kada a yi babban taron APC na ƙasa a ranar 26 ga watan Maris kamar yadda a ka tsara.
El-Rufai ya ce Buhari ya faɗa musu cewa lallai Abubakar Sani Bello ya karɓe jam’iyar nan kuma ya Banu umarnin a yi duk abin da ya dace a tabbatar an yi babban taron APC a ranar 26 ga Maris.
Ya kuma yi zargin cewa har umarni Buni ya samo da ga kotu domin hana wannan taron na APC amma sai ya ɓoye maganar.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button