Amarya ta mutu ana tsakiyar bikinta, sai aka zarce bikin da kanwarta
Wani bakon al’amari mai kama da shirin wasan kwaikwayo a kasar Indiya, wata amarya da ake tsaka da bikinta ta riga mu gidan gaskiya, to sai dai an yanke shawarar ci gaba da bikin da kanwarta.
Amaryar mai suna Surabhi ta mutu ne a yanki Etawah dake birnin Uttar Pradesh na kasar ta Indiya.
Majiyoyi da dama sun bayyana cewa bayan mutuwar Surabhi ne, yan uwa da iyalanta suka yanke shawarar jingine gawarta a wani daki dake kusa da nata kana aka ci gaba da raɓashewa.Kamar yadda jaridar dimokuradiyya na ruwaito.
Wani shaidar gani da ido ya tabbatar da cewa mutuwar tata ta biyo bayan wani cacar baki ta kaure tsakaninta da angonta mai suna Manjesh Kumar, nan take ne ta yanki jiki ta fadi.
Sai dai ba tare da wata-wata ba ne bayan wannan fadiwa tata bagatatan, likitoci suka garzaya kanta don bata kulawar gaggawa, to amma an ce idan ajali ya yi kira babu makawa sai an tafi, nan ne fa ta ce ga garinku.
A tsokacinsa, kawun amaryar da ta rigamu gidan gaskiya mai suna Ajab Singh, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Indiya wato IANS cewa sun yanke shawarar haɗa Kumar da kanwar amaryar ce ganin yadda suke buƙatar kulla dangantaka tsakanin su.
Karanta wannan labari :
Har yanzu ana ya yi na a masana’antar Kannywood – Fati Bararoji
Da dumi dumi : Buhari zai tafi London don duba lafiyarsa
“Yar mu ɗaya ta mutu a wani daki, sai muka yanke shawarar ci gaba da bikin da kanwarta, ba mu taɓa ganin haka ba a tarihi”
“Juyayin mutuwa da kuma farin cikin bikin sun kasa gaurayuwa a lokaci guda” kamar yadda kawun amaryar ya tabbatar.
Ya kara da cewa wani ɗan uwa ne ga iyalansu ya bijiro da shawarar haɗa wannan aure duba da doguwar zumunci dake tsakanin ahalinsu, nan da nan aka tattauna tare da cimma matsaya.
Kuma tuni labarin auren Nisha da Kumar ya karade shafukan sada zumunta na zamani yayin da mutane sama miliyan 260 suka duba labarin.