Turkiyya za ta ayyana makokin kwana uku a kasarta don alhinin abin da ya faru a Gaza


Majalisar dokokin Turkiyya ta yi Allah wadai da hare-haren Isra’ila a kan asibitoci a wata sanarwar hadin gwiwa, tana mai cewa kai wa cibiyoyin lafiya hari ya take dokokin yaƙi na ƙasa da ƙasa,
Turkiyya za ta ayyana makokin kwana uku a ƙasarta don taya Falasɗinu alhini bayan harin saman da Isra’ila ta kai kan Asibitin Al Ahli Arab da ke Gaza wanda ya yi sanadin mutuwar aƙallam mutum 500.
Za a sanar da wata doka ta shugaban ƙasa a matsayin martani ga hare-haren da Isra’ila take kai wa Gaza babu ƙaƙƙautawa, a cewar wata ƴar majalisar Turkiyya kuma mataimakiyar shugaban Jam’iyyar AK mai mulki, Ozlem Zengin, a ranar Laraba.


Ta ƙara da cewa majalisar dokokin a wata sanarwa ta haɗaka ta yi Allah wadai da hare-haren Isra’ila a kan asibitoci, tare da jaddada cewa kai hari kan cibiyoyin lafiya abu ne da ya saɓawa dokokin yaƙi na ƙasa da ƙasa.jaridar TRTAFRIKA Hausa na ruwaito.
Harin ya janyo Allah wadai da kakkausar murya daga Turkiyya, inda Shugaba Recep Tayyip Erdogan ya yi kira ga dukkan ƴan’adam da su ɗauki matakin dakatar da Isra’ila daga kai hare-haren “da ba a taɓa gani ba da mugunta a Gaza.”
“Kai hari kan asibiti inda mata da yara da fararen hular da ba su ji ba, ba su gani ba suke, babban misali ne na hare-haren Isra’ila na take hakki da darajar ɗan’adam,” kamar yadda Erdogan ya wallafa a shafinsa na X.
“Kai hari a kan asibiti mummunan laifi ne. Yi wa mutanen da ke kwance suna jinya kisan kiyashi ya shallake tunani. Kai hari kan fararen hula amfani ne da dabarun ta’addanci, gaskiyar magana kenan,” kamar yadda Daraktan Sadarwa na Turkiyya Fahrettin Altun shi ma ya wallafa a shafinsa na X.