Kannywood

Har yanzu ana ya yi na a masana’antar Kannywood – Fati Bararoji

Fati Baffa

• “Kwana biyu da akaji ni shiru harkokin kasuwanci ne suka da bai baye ni” inji ta.
• Fati ta kuma yi kira ga masoyanta da su cigaba da bibiyar fina-finan ta manyan tashoshin talbijin.
Tsohuwar jaruma a masana’antar fina-finai ta Kannywood Fati Baffa Fagge, wacce a ke wa lakabi da Fati Bararoji. Ta bayyana cewar ita fa har yanzu ba ta yi tsufan da za a daina yayin ta ba a cikin masana’antar, domin kuwa, har yanzu a na damawa da ita kamar lokacin kuruciyar ta.
Jarumar ta bayyana hakan ne a lokacin tattaunawar su da wakilin jaridar Dimokuradiyya, dangane da har yanzu irin su da suka dade a harkar ba su matsu, sun bar wa yan baya ba, da suka shigo harkar a yanzu, kasancewar su jaruman da suka ci lokacin su a baya.
DUBA WANNAN LABARIN:‘Yar Shekaru 21 Ta Kashe Biloniya Mai Shekaru 50 A Gidan Shi (hotuna da bidiyo)
Sai dai Jarumar ta yi saurin bada amsa da cewar “Sam babu wani lokacin mu da za a ce mun ci a baya, kuma yanzu mun zo muna cin na wasu, domin babu wanda ya ke cin lokacin wani, don haka yanzu ma lokacin mu ne.” Inji ta.
Fati baffa (bararoji)

Ko da muka tambaye ta dalilin da ya sa ba a fiye ganin ta ba sosai, sai ta ce “Ai da ba a gani na, ba Wai na daina fim ba ne, wasu harkokin kasuwancin da na ke yi ne, su ka sa ba a gani, don kada na karbi aikin mutane ya zama ban samu zuwa ba, Amma da ya ke a yanzu ina samun lokaci ai ga shi ana gani na, don haka babu wani-daina yayin mu da aka yi, kuma har yanzu muna cin lokacin mu ne.” Kamar yadda ta ce
Daga karshe ta yi kira da masoyan ta da su ci gaba da kallon fina-finan da za su fito nan gaba, domin za su ci gaba da ganin ta musamman fina-finan da a ke haskawa a gidajen talbijin manya, irin su Arewa 24 da sauran su.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button