Labarai

Takaitaccan jawabin sarkin Kano Muhammad Sanusi ll akan batun rufe boda da sanya harajin VAT

Daga Anas Saminu Ja’en

A zantawarsa da manema labarai game da tattalin arziki mai martaba sarkin Kano Muhammad Sanusi ll ya fara da cewar, na farko dai idan aka duba sauran kasashe da muke tsari irin na mu idan aka duba Amerika misali shugaban kasar Amerika kullum yana da tsari na kwamiti masu bashi shawara akan tattalin arzikin kasa, kyau duk da shugaban kasa yana da ministan kuda yana da gwamnan babban banki yana bukatar masu ilimin tattalin arziki su bashi shawara shima yasan abun da ya kamata a yi, kuma wannan mataki da shugaban kasa ya dauka matakine wanda ya dace musamman wannan lokacin da muke matsalolin tattalin arziki na duniya suke fuskantar matsaloli ana bukata a wannan lokacin ai shiri mai kyau saboda kare tattalin arzikin Najeriya, babban abun da muka lura da shi shi ne dukkannin mutanan da aka zaba mutanene masu cikakken ilimi a fannin su.

Kuma sarki ya yi karin haske game da rufe bodoji a daidai lokacin da ‘yan kasa ke kokawa.

To ai rufe hanyoyi da aka yi wani abu ne da ya zama dole saboda su kasashen da kewaye da mu basa kiyayewa wajan kare tattalin arzikin kasar nan, yanzu misali idan ana so a kare manoman mu na shinkafa kuma saboda a kare su a saka haraji mai tsauri akan shinkafa da ake shigo da ita daga waje, kasar da ta bari ana shigo da shinkafa ba a biya wannan harajin ba cutar manoman mu take saboda ana shigo da shinkafa mai araha da zata hana manoman mu ribar abun da suka shuka me zai sa mu ci gaba da shigo da shinkafa kasar nan, kuma za a tuna lokacin da shugaban kasa Janar Buhari yazo nan Kano wata ziyara jawabin da na yi a gidan gwamnati na bashi shawara tun lokacin a rufe wannan iyakokin lokacin shi ne yace a’a ya kamata kara hakuri dan haka wannan rufewar watakila bama da son ransa aka rufe ba.

Amman mu tuntuni muka ce a rufe saboda idan ba a rufe ba ba za a wato abun da ake bukata na buri ba, akwai fetur wanda saboda tallafi da ake bayarwa a nan Najeriya daga nan sai a shigo da shi gwamnatin tarayya ta biya tallafi sai a dauki feturin ba a siyarwa ‘yan Najeriya sai a dauki feturin a kai shi waje a siyar da shi da tsada, ya zama wato gwamnatin Najeriya take ba da tallafi ba na ‘yan  Najeriya na dukkanin ‘yan West African saboda haka rufe bodar nan gaskiya zai taimaka wajan kawo gyara cikin abubuwa da suke kawomana gibi a cikin kasar mu.

Kuma da yawa idan gwamnati ta kawo wani tsari talaka yana son ganin ya amfana, shima sarki ya ce wani abu akai cikin kankanan lokaci.

Eh! to abun da ya kamata a yi koda yaushe shi ne al’umma su ci gaba su gwamnati da kuma wadanda suka fahimci abun da yasa aka yi a ci gaba da bayani, yanzu misali kwanannan an kawo karin haraji VAT daga kashi 5 cikin 100 zuwa kashi 7 cikin 100 idan aka duba dukkan kasar da suka kewaye mu babu kasar da VAT dinnan yana kasa da 10 cikin 100 ko kashi 15 cikin 100 to mu da muke Najeriya abun da muke karba a cikin haraji gabaki daya kashi 6 cikin 100 na wato kasar waje a duniya muna cikin kasashe mafi kasa, idan ba a biya haraji ba ina za a saka kudi a cikin harkar ilimi ina za a saka kudi harkar lafiya yanzu ‘yan Najeriya sun ce suna son tallafin mai tallafin man nan biya ake yi idan ba a biya haraji ba ina gwamnati zata bayar da kudin tallafin mai zata bayar da tallafin kudin lantarki ina zata bayar da taimako na ciyar da yara a makarantu saboda haka ya kamata su mutanan Najeriya su san cewar ana bukatar mutanan kasa su bayar da haraji dan gwamnati tasan abun da zatai musu, kuma shi wannan harajin shi zai rage bashin da gwamnati take ci kuma shi ne zai bar gwamnati da zata samu hanyar da zata saka akan abun da yake ha amfanin al’umma wani abun kuma ana hakuri da jin dadin yau saboda gobe yanzu misali kudin da aka saka a cikin ilimin yara ai yara za su amfana da shi gobe shi mahaifi yana ganin baiga amfanin sa ba yau amman nan gaba zai ga amfanin sa saboda ilimin yara ne.

Me za Ku ce

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button