Labarai

Wata sabuwa ! Nayi Nadamar Kafa Rundunar SARS ~ Fulani kwajafa

Bbchausa hausa tayi fira da mutumin da ya kafa rundunar SARS da ke yaki da fashi da makami a Najeriya ya ce ya yi nadamar kafa ta sakamakon zarge-zargen da ake yi wa dakarunta na cin zarafin jama’a.
A makon jiya ne Babban Sifeton ‘yan sandan kasar ya sanar da rusa rundunar bayan an gudanar da jerin zanga-zanga a wasu yankunan kasar domin yin tur da gallazawar da jami’an rundunar suka kwashe shekara da shekaru suna yi wa ‘yan Najeriya.
Tuni gwamnatin ta kafa wata sabuwar rundunar mai suna SWAT don maye gurbin SARS, ko da yake matakin ga alama bai gamsar da masu zanga-zangar ba.
A 1984 ne dai, aka kafa rundunar ta SARS – jim kaɗan bayan hawan Shugaba Muhammadu Buhari kan mulkin soji.
Tsohon kwamishinan ‘yan sanda, Fulani Kwajafa, shi ne ya jagoranci kafa rundunar a lokacin yana aikin.
Tsohon jami’in ɗan sandan wanda a yanzu ya zarce shekara tamanin ya shaida wa Ishaq Khalid cewa yakan yi da-na-sani, da ya jagoranci kirkiro rundunar ta SARS saboda ƙaurin sunan da ta yi a baya-bayan nan kan ayyukan ta’asa.
Ga bidiyo nan da bbchausa na zanta da shi zaku iya kallo.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button