Uncategorized
Mai shafin Twitter ya goyi-bayan zanga-zangar #EndSars
Mutumin da ya samar da shafin Twitter, Jack Dorsey ya nuna goyon-bayansa ga zanga-zangar #EndSARS da ke ci gaba da jan hankali a Najeriya
Dorsey ya sake wallafa bayanan asusun tara kuɗin tallafawa zanga-zangar a shafinsa @jack dauke da alamar tutar Najeriya.
Donate via #Bitcoin to help #EndSARS ?? https://t.co/kf305SFXze
— jack (@jack) October 14, 2020
Sannan ya sake wallafa wasu maƙaloli da ke nuna goyon-bayan zanga-zangar.
— jack (@jack) October 14, 2020
Sai dai wannan alamari ya janyo yabo da suka a shafin na sadarwa abin da ya kai ga wani mamba a Jam’iyyar APC, wanda kuma ya taɓa neman takara shugaban ƙasa Adamu Garba barazanar kalubalantarsa a kotu inda zanga-zangar ta kazance.tattara bayyanai bbchausa