Labarai

Matar Da Ake Zargi Ta Kashe Ƴaƴanta A Kano Tana Da Aljannu

Mahaifiyarta matar da ake zargi ta kashe ƴaƴanta guda biyu a jihar Kano da ke Najeriya ta ce ‘yarta ta daɗe tana rashin lafiyar da ke da nasaba da iskokai.
A ranar Asabar ne rundunar ‘yan sandan Jihar Kano ta tabbatar da mutuwar wasu yara biyu mace da namiji yan shekara uku da kuma shida da ake zargin mahaifiyarsu ce ta kashe su.
Lamarin wanda ya faru a Unguwar Sagagi Layin ‘Yan Rariya a birnin Kano, da farko an bayyana cewa sabani ne da mijinta saboda ya yi mata kishiya a watannin baya ya kai ga kisan ƴaƴansu.
Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta ce jami’anta sun kama matar yanzu haka tana hannunsu, kuma ta tabbatar da cewa ita ta kashe ƴaƴanta, kamar yadda kakakin rundunar ya shaida wa BBC.
Ya kuma ce bayan matar ta kashe yayanta uku ta kuma raunata wata yarinya yar shekara 10.
Amma kakar yaran da aka kashe Binta Ado Nababa ta shaida wa BBC cewa ƴarta ta shafe tsawon wata uku ba ta iya bacci, “tana cewa kullum da dare ana zuwa ana danne ta ana shake ta. Ta fi wata uku ba ta bacci, da dare ana yi mata gurnani irin na dodanni.Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button