Labarai
Buhari Ya Haramta Alfarma Wajen Neman Aiki
Advertisment
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sake jan kunnen masu riƙe da muƙaman siyasa da sauran ma’aikatan gwamnati da su guji amfani da matsayinsu wurin nemo aiki ga waɗanda suke so.
A wata sanarwa da ministan yaɗa labarai da al’adu Lai Mohammed ya fitar, shugaban ya ce wannan ɗabi’ar ta saɓa wa dokar gudanarwa ta aikin gwamnati.
Sanarwar ta ce gargaɗin na shugaban ƙasar ya biyo bayan rahotanni da ake yawan samu kan yadda manyan ma’aikatan gwamnati da masu muƙaman siyasa da masu taimaka wa shugaban ƙasa ke amfani da katinsu ko kuma rubutacciyar wasiƙa wajen neman aiki da kuma kwangiloli.
Ministan ya ce hukumomi da ma’aikatu su yi watsi da duk wasu buƙatu da wani jami’in gwamnati ya turo musu na neman aiki ko kuma kwangila ga wani.
Ya ce gwamnati ta fitar da tsare-tsare da hanyoyin da ya kamata a bi wajen bayar da aiki ko kuma kwangila.
Rashin aikin yi a Najeriya na ɗaya daga cikin matsalolin da suka addabi jama’ar ƙasar musamman matasa.
Dubu daruruwan matasa ne ke kammala karatun jami’a a duk shekara a ƙasar ba tare da samun ayyukan yi ba.
Abu na farko da matasa kan yi bayan kammala jami’a ko kuma kwalejojin ilimi ko na kimiyya shi ne rarraba takardun shaidar kammala karatunsu zuwa ‘yan uwa da abokan arziƙi domin neman aiki.
Ana yin hakan ne sakamakon ammanar da aka yi da cewa ba a samun aiki a Najeriya sai an san wani ko kuma sai idan mutum na da “ƙafa”.
A Najeriya idan aka ce mutum na da ƙafa ko kuma doguwar ƙafa, ana nufin mutum ya san wani hamshaƙi ko kuma mai faɗa a ji ko kuma wani da ke da hanyar samo masa aiki ko kuma kwangila.
A wannan dalili ne ya sa waɗanda ba su da “kafa”, kamar yadda ake faɗa suke rasa ayyukan yi, sai dai kaɗan daga cikin waɗanda Allah ya nufa da samun aiki.
Akwai wasu manyan ma’aikatu a ƙasar masu biyan albashi mai tsoka da mutane da dama ba su karambani wajen neman aiki a irin waɗannan wurare. Hakan na faruwa ne domin tuni an yi ammanar cewa idan baka san wani babba a ma’aikatun ba ko kuma a ƙasar, ba za ka samu aiki ba.
A baya-bayan nan sakamakon yadda matsalar rashin aikin yi ta ƙara ta’azzara, jama’a da dama na ƙoƙrin neman aiki a ƙasar ko ta halin ƙa’ƙa ko da kuwa don su saya da kudinsu ne.
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com