Kannywood

Ba’a Kafa Nigeriya Don Gina Kasa Da Bunkasa Al’umma Ba ~ Aminu Ala

Bayan 1 ga watan Oktoba shekara ta dubu biyu da ashirin anyi bukin samun ‘yancin kai da kasarmu Najeriya ta samu shekara sittin kenan.
Wanda ankayi buki da murna wanda a ranar juma’a shahararren marubucin wakokin hausa wato Aminu Abubakar Ladan wanda ake ma lakabin da Alan waka yayi bayyani mai nuni da inda Nigeria ta dosa.
shahararren marubucin wakokin hausa ya wallafa wannan rubutun nasa a shafin na Instagram ga abinda yake cewa.
NIJERIYA ƙASATA
(BIRI DA MANDA)
Ƙasar Nijeriya tana a yammacin Afurika, kasa ce Mai Faɗin Murabba’in Mil dubu ɗari uku da talatin da tara.
Faɗinta ya zarci yawan Kasar faransa da italiya. a yayin da yawan Mutanenta ya zarci haɗaɗɗiyar daular Ingila bakiɗayanta.
Ba a kafa Nijeriya don gina kasa da bunkasa Al’umma ba. An kafa ta ne kaɗai don muradin kasuwanci na turawan Yamma da bukatunsu. Wannan ya na daga dalilin da ya kawo rabuwar kai na kabilun cikinta, kowanne ɓangare ya na rajin neman yanci kai a bangarensa ba a Haɗaɗɗiyar Nijeriya bakiɗaya ba.
Kamar yarda kasar take da yalwar Faɗin ƙasa da yawan Mutane, haka take da yawan ma’adanai na Albarkatun ƙasa nau’i-nau’i kama daga kudancin kasar zuwa Arewacin kasar bakiɗaya.
Ba a iyaka Afurka kaɗai ba ko a tarayyar Turai ba ko wacce kasa za a gwada ta da Nijeriya ba a wajen Nau’i na arzikin albarkatun kasa.
MAMMORA:
Gallar arzikin da Allah kan baiwa kasashe don su ci Moriya daga Ni’imar da aka ni’imtasu da ita, Kasar Nijeriya ta sami Tasgaro da jagorori Marasa kishin kasa da babakere da handama. A rana irin ta yau ake bikin Murnar zagayowar ranar da aka sami ‘Yancin kai. Amma har kawo yanzu kasar tana a matakin samar da wajiban abubuwan gudanar da kasa ne ba a kai ga gina kasa da Al’umar kasa ba.
Akwai waɗansu ginshiƙan matsaloli da suka zama wajibin kowacce Al’uma ta same su don suna daga farillan rayuwa da suka haɗa da:
*-Tsaron Rayuka da Dukiya,
*-Wutar Lantarki Don gudanar da Ƙasa,
*-Ilimi Don ɗora al’uma akan tafarkin Shari’a da ingattacciyar Rayuwa,
*-Samar da Hukumomin lafiya da Ingantattun Asibitocin kula da lafiya,
*-Hanyoyin Sufuri da suka hada da na sama da kasa da na ruwa don inganta harkokin kasuwanci da bunkasa tattalin arziƙi,
Matsalar Tattalin arziki.
Komai lalacewar kasa ya kamata ‘Ya’yanta su fi karfin waɗan nan Ginshikai na rayuwa. Amma a kasar Nijeriya wadannan sun gagara ba don komai ba sai dalilin ‘yan wa-ka-ci-ka-tashi.
Kamar da gayya tsaron Nijeriya ke tafiya a halin da ya ke, ba domin komai ba sai don ana sane da cewa Jami’an tsaron kasar na ko wanne janibi sun kasawa Adadin yawan Jama’ar Kasar Balle su samar da kariyar rayuwa da dukiyar jama’a Balle uwa uba kishin ƙasa.”

 

View this post on Instagram

 

NIJERIYA ƙASATA (BIRI DA MANDA) Ƙasar Nijeriya tana a yammacin Afurika, kasa ce Mai Faɗin Murabba’in Mil dubu ɗari uku da talatin da tara. Faɗinta ya zarci yawan Kasar faransa da italiya. a yayin da yawan Mutanenta ya zarci haɗaɗɗiyar daular Ingila bakiɗayanta. Ba a kafa Nijeriya don gina kasa da bunkasa Al’umma ba. An kafa ta ne kaɗai don muradin kasuwanci na turawan Yamma da bukatunsu. Wannan ya na daga dalilin da ya kawo rabuwar kai na kabilun cikinta, kowanne ɓangare ya na rajin neman yanci kai a bangarensa ba a Haɗaɗɗiyar Nijeriya bakiɗaya ba. Kamar yarda kasar take da yalwar Faɗin ƙasa da yawan Mutane, haka take da yawan ma’adanai na Albarkatun ƙasa nau’i-nau’i kama daga kudancin kasar zuwa Arewacin kasar bakiɗaya. Ba a iyaka Afurka kaɗai ba ko a tarayyar Turai ba ko wacce kasa za a gwada ta da Nijeriya ba a wajen Nau’i na arzikin albarkatun kasa. MAMMORA: Gallar arzikin da Allah kan baiwa kasashe don su ci Moriya daga Ni’imar da aka ni’imtasu da ita, Kasar Nijeriya ta sami Tasgaro da jagorori Marasa kishin kasa da babakere da handama. A rana irin ta yau ake bikin Murnar zagayowar ranar da aka sami ‘Yancin kai. Amma har kawo yanzu kasar tana a matakin samar da wajiban abubuwan gudanar da kasa ne ba a kai ga gina kasa da Al’umar kasa ba. Akwai waɗansu ginshiƙan matsaloli da suka zama wajibin kowacce Al’uma ta same su don suna daga farillan rayuwa da suka haɗa da: *-Tsaron Rayuka da Dukiya, *-Wutar Lantarki Don gudanar da Ƙasa, *-Ilimi Don ɗora al’uma akan tafarkin Shari’a da ingattacciyar Rayuwa, *-Samar da Hukumomin lafiya da Ingantattun Asibitocin kula da lafiya, *-Hanyoyin Sufuri da suka hada da na sama da kasa da na ruwa don inganta harkokin kasuwanci da bunkasa tattalin arziƙi, Matsalar Tattalin arziki. Komai lalacewar kasa ya kamata ‘Ya’yanta su fi karfin waɗan nan Ginshikai na rayuwa. Amma a kasar Nijeriya wadannan sun gagara ba don komai ba sai dalilin ‘yan wa-ka-ci-ka-tashi. Kamar da gayya tsaron Nijeriya ke tafiya a halin da ya ke, ba domin komai ba sai don ana sane da cewa Jami’an tsaron kasar na ko wanne janibi sun kasawa Adadin yawan Jama’ar Kasar Balle su samar da kariyar rayuwa da dukiyar jama’a Balle uwa uba kishin ƙasa.

A post shared by ALAN WAKA (@alan_waka) on

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button